Majalisar Tarayya: Kotu ta tabbatar da nasarar ɗan takarar NNPP a Kano

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Majalisar Tarayya da ta jiha, ta tabbatar da nasarar ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, Mudassir Zawachiki, a matsayin wakilin al’ummar Kumbotso a Jihar Kano a Majalisar Wakilai ya Tarayya.

Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a L. B. Owolabi, ya yi watsi da ƙarar da Sagir Abdulkadir-Panshekara na Jam’iyyar APC ya shigar inda yake ƙalubalantar nasarar Zawachiki a zaɓen da ya gudana ran 18 ga Maris, 2023.

Kotu ta ce mai ƙarar ba shi da hurumi kuma ya kasa gabatar da hujjoji kan cewa an yi arigizon ƙiri’u, tada zaune tsaye da amfani da takardun bogi yayin zaɓen.

“Mai ƙara ya gaza kare ƙorafinsa na cewa an yi wa Dokar Zaɓe ta 2022 karan tsaye da sauran matsaloli,” in ji kotun.

Da yake tofa albarkacin bakinsa jim kaɗan bayan yanke hukunci, Zawachiki faɗa wa manema labarai cewa, “Ina godiya ga Allah Maɗaukaki da gaskiya ta yi halinta. Zan ci gaba da yin ƙoƙarina wajen yi wa yardar da jama’a suka ba ni adalci.”