Majalisar Tattalin Arziƙi ta buƙaci gwamnatocin jihohi su amince da shirye-shiryen kula da tsarin samar da abinci na Shugaban ƙasa

 
Daga BELLO A. BABAJI

Hakan na zuwa ne a lokacin da Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, irin tattalin arziƙin da gwamnatin tarayya ta shuka ta hanyar kawo sababbin tsare-tsare da bayar da tallafi a shekarar 2024 ya fara yin ƴaƴa.

Majalisar Tattalin Arziƙin Ƙasa (NEC) ta ɗauki matakin ne a ranar Alhamis, yayin taronta na 147 da mataimakin shugaban ya jagoranta a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Yayin gabatar da jawabinta, mai taimaka wa shugaban ƙasa kan dabarun noma a ofishin mataimakin shugaban kasa, kuma shugabar sashin kula da tsarin samar da abinci na shugaban ƙasa, Marion Moon, ta yi karin haske kan dabarun da sashin ya gabatar don yin aiki tare da gwamnatocin jihohi wajen magance matsalar ƙarancin abinci da kuma bunƙasa harkokin noma a faɗin Nijeriya.

Marion ta ce shirin sashin Kula da Tsarin Abinci na Shugaban Ƙasar (PFSCU) zai mayar da hankali ne a ɓangaren bunƙasa kasuwancin amfanin gona, da hakan zai taimaka wajen inganta hanyoyin isar da kayayyaki haɗi da hanzarta aiwatar da manufofin da aka sanya acikin shirin sabonta fata (Renewed Hope) na gwamnatin Shugaba Tinubu da kuma cimma manufofin gwamnatocin jihohin.

A nata bangaren, NEC ta yaba da jawabin na shugabar shirin, yayin da ta yi kira ga gwamnatocin jihohi su shiga cikin wannan shiri.

Har’ilayau, majalisar ta buƙaci PFSCU da su gabatar da nasarorin da suka samu a taron majalisar na gaba.