Majalisar Wakilai ta amince wa Buhari karɓar bashin N368bn daga Bankin Duniya

Majalisar Tarayya ta Ƙasa ta amince wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ya kinkimo bashin Naira biliyan 368.7 (Dala miliyan 800) daga Bankin Duniya.

Mamba a Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sha’anin Bashi da Tallafi, Abubakar Yunusa Ahmad, shi ne ya bayyana haka a wani shiri da Tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Juma’a.

Sai dan majalisar ya ce ba za a yi amfani da bashin ba a gwamnatin Buhari mai ƙarewa. Yana mai cewa, gwamnati mai jiran gado ce za ta sarrafa bashin don cimma manufar da ta sa aka ciyo shi.

A cewarsa, game da Dala miliyan 800, “Mun tattauna sosai, musamman ma mu da muke cikin Kwamitin ɗauko bashi, mun shawarce su a kan su sakar wa gwamnati mai zuwa lamarin.

“Amma tun da an amince da karɓar bashin muna iya karɓa. Idan ba za mu iya amfani da kuɗin ba, wataƙila idan gwamnati mai zuwa ta shigo za ta san yadda za ta sarrafa bashin.

“Batun dai shi ne mun amince da bashin, muna so ‘yan Nijeriya su karɓe shi, sai dai ba za a yi amfani da kuɗin a wannan gwamnati mai barin gado ba,” in ji Ahmad.