Daga USMAN KAROFI
Majalisar Wakilan Nijeriya ta ɗage tattaunawa kan muhimman dokokin gyaran haraji da ake taƙaddama akansu har sai wani lokaci.
Dokokin huɗu sune dokar harajin Nijeriya ta 2024, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji ta Nijeriya da kuma dokar kafa kwamitin haɗin gwiwa na haraji sun samu suka daga ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da ƙungiyar gwamnonin Arewa, majalisar sarakunan gargajiya, kwamitin tattalin Arziki na Ƙasa, da kuma ƙungiyar dattawan Arewa.
Kwamitin tattalin arziki na ƙasa, wanda ya ƙunshi mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni, ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya janye dokokin tare da ba da damar ƙarin tuntuɓa.
Gwamnonin sun ce wasu sassa na dokokin na barazana ga yankin Arewa.
Duk da wannan adawa, dokokin huɗu sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa. Amma a Majalisar Wakilai, rikici ya ɓarke yayin tattaunawa, inda ‘yan majalisar suka ƙi yarda da matsin lamba daga shugabannin majalisar don su amince da dokokin.
Bayan taƙaddama mai zafi, majalisar ta ɗage zaman har zuwa 3 ga Disamba domin ƙarin tattaunawa da Taiwo Oyedele shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin Kuɗi da gyaran haraji, don ƙarin a wuraren da ake samun saɓani a cikin dokokin.
Sai dai wata takarda da aka gani, wanda aka sanyawa hannu a ranar 30 ga Nuwamba daga akawun majalisar wakilai, Yahaya Ɗanzaria, ya nuna cewa an sake ɗage wannan zaman na musamman zuwa wani lokaci nan gaba