Majalisar wakilai ta gabatar da ƙudurin wa’adin mulkin shekara shida ga Shugaban ƙasa da gwamnoni.

Wata ƙungiyar ‘yan majalisar wakilai 35 ta gabatar da ƙudurin wa’adin mulki na shekaru shida ga Shugaban ƙasar Najeriya da ma gwamnonin jihohi.
‘Yan majalisar sun kuma ya ce ya kamata a riƙa gudanar da zaɓukan muƙaman siyasa a rana guda, don kuɓutar da ƙasar daga kashe maƙudan kudaɗe wajen gudanar da zaɓe.
Mai magana da yawun ƙungiyar, Hon., Ikenga Imo Ugochinyere, wanda ya jagoranci sauran mambobin ƙungiyar, ya bayyana shida daga cikin ƙudurin doka hamsin, wanda wasu daga cikinsu sun riga sun tsallake karatun farko, a yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin.