Majalisar Wakilai ta karɓi buƙatar Buhari kan neman ƙarin kasafi na bilyan N896

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar Talata Majalisar Wakilai ta Tarayya ta karɓi bukatar Shugaban Ƙasa Muhammadu kan buƙatar neman ƙarin kasafin 2021 da ya gabatar.

Buhari ya buƙaci ƙarin kasafi na Naira bilyan 895.8 ne domin yauƙaƙa kasafin 2021.

An ce ƙarin kasafin da Buhari ya nema za a a yi amfani da shi ne wajen ƙara wa sojoji kayan aiki da bunƙasa shirin rigakafin korona da na yaƙi da cutar HIV.

A makon da ya gabata Majalisar Datawa ta yi nazarin buƙatar ƙarin kasafin da Shugaba Buhari ya gabatar mata a mataki na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *