Majalisar Wakilai ta umarci a kama daraktan kwalejin koyon tuƙin jirgi kan sayar da helikwaftan Dala 1.2

Daga Farouk Abbas

Kwamitin kadarorin ƙasa na Majalisar wakilai ya buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta kama daraktan kwalejin koyon tuƙin jirgin sama da ke Zariya kan sayar da helikwafta guda biyu a dala miliyan 1.2.

Kwamitin ya yi kira ga sufeta Janar na Rundunar Ƴan sanda, Kayode Egbetokun da ya yi bincike kan sayar da helikwaftocin da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

Shugaban kwamitin, Ademorin Koye, yayin wani dogon zama da wakilan hukumar kwalejin, ya nuna damuwa kan lamarin inda ya bukaci a yi bincike.

An sayo jiragen kan dala miliyan 2.4 yayinda aka ce an sayar da su a dala miliyan 1.2 ba bisa ƙa’ida ba kamar yadda Ademorin ya ce.

Ademorin ya ƙara da cewa, kwamitinsu ya na buƙatar jadawalin dukkan abubuwan da kwalejin ya mallaka da bayanai a kansu ta yadda za su tantance su a dokance.