Majalisar Wakilai za ta hana aikin jarida ga marasa digiri

Daga BASHIR ISAH

A matsayin wani mataki na neman tsaftace aikin jarida a Nijeriya, Majalisar Wakilai ta soma nazarin ɗaga shaidar zama ɗan jarida zuwa digiri na ɗaya ko HND ko makamancin haka a aikin jarida.

Buƙatar hakan ta taso ne biyo bayan ƙudirin da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ado/Ogbadigbo/Okpokwu, Francis Agbo ya gabatar a gaban majalisar na neman yi wa dokar aikin jarida kwaskwarima, wato Nigerian Press Council Amendment Bill 2019.

Tuni dai wannan ƙuduri ya tsallake matakin nazari na ɗaya ake kuma shirin nazarinsa a mataki na biyu inda ake buƙatar yi wa dokar aikin jaridar, wato Act Cap N128 LFN 2004 kwaskwarima.

Ta ce duk mai buƙatar shiga aikin jarida a Nijeriya “dole ne ya zamana yana da shaidar digiri na ɗaya, ko shidar Babbar Difloma (HND) ko makamancin haka a fannin aikin jarida ko danginsa daga makarantar gaba da sakandare a ciki ko wajen Nijeriya.”

Haka nan, dokar ta ce idan kuwa mutum na da shaidar digiri ta ɗaya a wani fannin na daban, “sai ya nemo satifiket ɗin sahalewar aikin jarida a tskanin shekaru biyar a ciki ko wajen Nijeriya.”

Mai taimaka wa Hon Agbo kan sha’anin yaɗa labarai, Andrew Agbese, ya ce dokar za ta taimaka wajen tsaftace aikin jarida daga ayyukan gurɓatattun ‘yan jarida.

Agbese ya ci gaba da cewa, “Dokar ta ja hankali sosai a fagen harkar yaɗa labarai duba da yadda ake fama da ‘yan jarida na bogi da masu yi wa aikin kutse wanda hakan kan kassara martaba da kimar ‘yan jarida na ƙwarai a ƙasar nan.

“Idan dokar ta tabbata za ta yi aiki qwajen kawar da ƙalubalan da aikin na jarida ke fuskanta tare da inganta masana’antar aikin jarida da ƙarfafa dimokuraɗiyya wanda hakan ya sa akwai buƙatar tantance halastattun ‘yan jarida daga na bogi, gami da hukuncin da za a yi wa duk wanda aka kama da karya dokar da masu yi wa aikin jarida kuste.”