Majalisar Zartarwa ta nemi a janye ƙudirin neman yi wa haraji kwaskwarima

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Zartarwa kan Tattali (NEC) ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ta nemi a janye ƙudirin da ke neman yi wa haraji kwaskwarima, wanda aka gabatar a Majalisa.

Acikin mambobin NEC akwai gwamnoni inda ɗaya daga cikin su wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Oyo, Sheyi Makinde ya bayyana wa manema labarai cewa an samu cecekuce ne kan ƙudirin wanda hakan ya sa suka ga dacewar a janye shi tare da sanya masu-ruwa-da-tsaki acikin lamarin.

Hakan na zuwa ne yayin ake tafka muhawara kan harajin VAT wanda a mafiya yawancin jihohin Arewacin Nijeriya da ake da shari’ar Muslunci, an haramta kasuwancin giya wanda kuma duk da haka su na ƙarbar wani kaso daga cikin harajin na VAT da ake samu.

Gwamnonin sun ce a halin yanzu ana bada kason VAT ne la’akari da inda kamfani ya ke ba inda ake amfani da hajarsa ba.

Cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce sabon tsarin da aka zayyano cikin ƙudirin, ya ƙunshi samar da hanya da za ta zama ta amfanar da duka jihohin.

Ya ce, ƙudirin neman kwaskwarimar harajin na neman gyara rashin daidaito da ke cikin raba kuɗin da ake samu daga VAT.

Ya kuma bayyana cewa, za a yi gyare-gyaren ne don amfanin al’ummar ƙasa ba wai tauye wani ɓangare na ƙasar ba.