Makamashi: Ɓarayin zaune

Tare Da BASHIR MUDI YAKASAI

Ƙasahe masu albarkacin man fetur a Afirka da sauran ƙasashe masu tasowa a faɗin duniya suna fuskantar matsalar ɓarayin zaune.

Su wane ne ɓarayin zaune a waɗannan ƙasashe har da Nijeriya? Maganar gaskiya babu wata ƙunbiya-ƙunbiya su ne manya-manya kamfanoni da suke karakaina a dazuka da gavar tekuna da kuma duk inda hamada ta ke, wato dai dukkan guraren da ake kyautata zaton akwai man fetur da gas.

Suna kiran wannan sana’a da ‘exploration and production’, wato bincike da kuma samarwa. Su binciko akwai man fetur ɗin, kuma yawansa ya kai yawan yawan da zai kai ga “kwalliya za ta biya kuɗin sabulu? Wannan shi yake ba su lasisi na zaman durshen na baba-ta-gani. Tun a shekara ta 1930 Turawan yammacin Turai daga Birtaniya da Faransa da Jamus da Portugal suke yawo a kudu maso kudu da kuma bakin teku da ake kira da ‘Guif of Guinea’. Fahintar akwai mai da gas ya sa suka share gindin zama.

Saboda zaman lafiya a tsakaninsu, Ƙasar Birtaniya ta buɗe bayar da lasisi ga waɗannan kamfanoni masu ‘exploration’, inda aka ba wa kamfanin Shell wannan dama a shekara ta 1937. Tun a wancan lokaci, sauran kamfanoni suka biyo baya, kamar Chevron da Mobil da Total da Agip da Eif da Texaco da Phillips Oil da kuma BP, wato British Petrolem, wanda ya koma AP, wato Africa Petroleum.

Fetur lokacin mulkin General Murtala Ramat Muhammad:

Saboda rashin ɗa’ar BP, ya haɗa baki da ’yan ƙasa marasa kishin ƙasa suka kashe shi akan hanyarsa ta zuwa wajen aiki a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

Waɗannan kamfononi da muka ambata su ne ‘Ɓarayin Zaune’ ta amfani da ’yan ‘sane’ na ma’aikatan mashahurin kamfanin nan, Nigerian National Petroleum Company (NNPC), wanda Nijeriya ta kafa shi a shekarar 1973 da Dubri Oil Company Limited (DOCL), wanda aka kafa a shekara ta 1987 da kuma wasu ’yan sanen daga kamfanin nan Nigeria Liquefied Natural Gas Limited (NLNG), wanda aka samar da shi a shekara ta 1993, domin ya riƙa hada-hadar wani kamfani ɗan autansu da ake kira Tenoil Petroleum and Energy Services, wanda yake tafiyar da aikinsa tare da kamfanoni na ’yan ƙasa.

Banda ɓarayin zaune da ’yan sane da kuma ‘yan fashi da makami masu amfani da makamai wajen ɗibar mai ta fasa bututu su kwashi ɗanyen man fetur a bana kawai, wato shekara ta 2023, sun fasa bututu sama 150 kuma sun kashe mutane sama da 30. Bayan ga haka, babu wanda zai iya ƙiyasta yawan man da suka kwasa. Amma an tabbatar da cewa, Nijeria ta yi asarar sama da kashi 40 na yawan kuɗaɗen da ta ke hasashen samu.

Akwai kuma ɓerayen dinka da suke taka muhimmiyar rawa wajen varna ta kwasar wannan dukiya ta man fetur da gas. Waɗannan verayen dinka jiragen ruwan dako ne ya kawo su. Ana haɗa baki da rasa kunya veran tanka; wato ƙananan beraye na gida (ƙananan ma’aikata) da suke aiki wajen lodi, a nan suke funce na ƙara yawan man da aka umarce su su loda wa Jirgin dako, anan suke yin nasu.

Wato majiya mai ƙarfi ta shaida min ‘pump operator’ kan sami Naira 500,000 a mako. Idan ka je ‘night club’ k aga saurayi na wasa da kuɗi da kuma ’yan mata, kada ka yi wata tantama ‘pump operator’ ne a ɗaya daga cikin ‘tanker terminals’ dake Bonny ko Bonny Island ko Idoho ko Brass Rivers ko Penington ko Forcados ko kuma ESCravos da dai sauransu da ke jihohin Rivers da Delta da kuma Bayelsa.

Haka ma direbobin tanka masu ɗaukar man fetur da gas a daffo-daffo (depots) da suke barbaje a cikin ƙasa a nan ma ana yin wakaci-katashi da masu lodi da direbobin mota da yaransu da kuma masu gadi na ciki da wajen daffo.

Idan ka ji irin badaqalar da ake tafkawa a waɗannan gurare, sai dai kawai takabir; ‘Innalillahi wa inna ilaihir’raji’un!’, ba dai mutum ba!

Wannan ba ta tsaya a daffo ba, ta je har gidajen sayar da mai, wato tashoshin sayar da mai, inda su ma ’yan bumburutu suke cin tasu kasuwar da ‘station manager’, musamman ma lokacin da mai ya yi ƙaranci a gari.

Maganin duk wata matsala ita ce, sauka daga tubulin toka da aka gina wannan masana’anta akansa, domin kuwa matsalar man fetir da gas da kuma dangoginsu, matsala ce kamar gobara daga teku, wacce ta bazu izuwa gobarar daji.

Kamar yadda muka ambata tun farko cewa, ɓarayin zaunan da ake da su, sun fito ne daga manya-manyan kamfanoni na qasashen yammacin Turai da Amurka ta Arewa, wato USA da Kanada, mabiyansu su ne masu ruwa da tsaki a cikin ƙasa- attajirai, malaman addini, sarakunan gargajiya, ’yan tarkarda (elites), ’yan majalisu, masu shari’a da masu zartarwa (excecutives) har ma da masu rajin rayuwa da haƙƙin ɗan adam, wato dai ‘whistle blowers’.

Babbar matsalar ita ce, a matsayinka na shugaba, wa za ka tava ka kawar da shi, ta hana shi satar da yake yi? Kuma mu tuna da mutane irin su Tafawa Ɓalewa da Murtala Ramat Muhammad da Umaru Musa ’Yar’Adua da Sani Abacha da Ba’are Mai-Nasara da Kanar Khaddafi da kuma baya-bayan nan Muhammadu Bazoum.
Dukkan waɗanda muka ambata sun rasa rayukansu, saboda kawai sun ce a yi adalci ga ‘yan ƙasa. Hatta sojoji ’yan ta’adda qarqashin Jagorancin Kanar Manjo Amadou Abduramane, wanda Ƙasar Faransa ta aiko shi, don kawai ya ce zai tsinke dangantakar da take tsakaninsu wacce ta rage ’yar ƙalinan.

Shugabanni suna tsaka mai wuya akan wannan matsala ta cire tallafin man fetur, wanda muka tabbata babu shi, da ma can dabaru ne na ɓarayin zaune; idan suna son su kawo ruɗani wajen ƙarin farashi sai su zuga ‘yan takarda (elites) dake cikinmu, iyayenmu da muka ɗauka suna da ilimin zaman duniya. Mun ga wannan a shekara ta 2017 lokacin mulkin Goodluck Ebele Jonathan, wanda Gwamnan Babban Banki Nijeriya Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi ya zuga shi da ya cire tallafin man fetur, wanda daga bisani farashi ya tashi daga Naira 65 zuwa Naira 87 duk lita. Wannan batu shi ya kawo faɗuwar gwamnatin ta Jonathan.

Masu iya magana na cewa, ‘tarihi ya na maimaita kansa’. Waɗannan varayin zaune, wato kamfanonin Shell, Chevron, Mobil, Total, Agig, Eif da kuma Texaco da dai sauransu da namu na gida irin su Oando, Eterna, Sterling, Barbedos, Rainoil, Levern EDL, A. Y. Maikifi, A. A. Rano da dai sauransu sai an zauna da su, an wayar da kansu idan suka cigaba da amfani da kasuwa ita za ta faɗi farashi ba hankali ba kara ba, ba tausayi ba, ta taimako ba, ba zumunta da zaman tare ba, sai riba, kuma ribar ma ta fi uwar kuɗi, idan masifa ta kunno kai sai ta mamaye Afrka gabaɗayanta, wanda shi zai haifar da yaƙin duniya na uku, domin kuwa Rasha da China suna tare da Afirka, kuma Indiya da ƙasashen Larabawa da iraq da Iran da kuma Siriya za su bada nau’in tallafin.

A guji tsokanar Nijeriya, rura wutar yunwa da fatara da talauci babban haɗari ne ga Nijeriya, domin idan tura ta kai bango, wuta ce za ta dawo kanku. Ku sani Afirka ta gaji da bauta, musamman bauta ta yunwa da talauci da fatara da kuma jahilci na matasa, mata da kanan yara.

Saboda haka a dawo da farashin da kowa ya san ya kan ci riba, wato Naira 65 a duk lita, za a zauna zaman lafiya da walwala da kuma arziki. Idan kunne ya ji, jiki ya tsira!