Makamashi: Albarkatun ƙasa a Nijeriya

Tare Da BASHIIR MUDI YAKASAI

Allah Maɗaukakin Sarki ya albarkanci wannan ƙasa ta Nijeriya da albarkatun ƙarƙashin ƙasa, da kusan babu wata a afrika da zata yi gogayya da ita. Kasace da zata taka kowacce irinn rawa a kasuwar duniya a fannin albarkatun ƙarƙashin ƙasa kamar Azurfa da tagulla da tama da kuza da zinariya da lu’u-lu’u da kuma uwa- uba ɗanyan man fetur da gas da kuma dangoginsa.

Tun bayan yaƙin duniya na biyu, ƙasar Birtaniya uwar gijiyar wannan ƙasa ta Nijeriya take kwasar wannan garabasar a gurare daban-daban, kamar tama da kuza a yankin Jos a jahar filato da gorar ruwa, wato ‘Columbite/Tantalate’ harshen kimiyya a ruruwai a ƙaramar hukumar Doguwa a jihar Kano da zinariya a jihar Adamawa da Taraba da Zamfara da kuma Jirahr Kebbi.

Haka an kwashi miliyoyin ton na makamashin kwal – ‘Coal’ Daga Jahohin Inugu Anambra da Imo da kuma Abia.

Baya ga Haka, Daga 1950, Jihar Delta Bayelsa da kuma Rivers da Akwa ibom, Kamfanonin wannan ƙasa ta birtaniya da na Faransa da kuma na Amurika Suke wadaƙa da miliyoyin gangar ɗanyen man fetur da gas da suke kwasa zuwa kasuwar duniya suna bamu ladan gabe da sunan bamu da ilimin sarrafa wannan hajar.

Godiya ta musamman ga mutane irin su janar Murtala Ramat Muhammad, wanda yayi mulki daga 29 ga watan yuli, 1975 zuwa 13 ga watan Fabereru na shekara ta 1976 inda ya kori Kamfanin BP, Wato British Petroleum, Mallakar Birtaniya ya mayar dashi AP, wato African Petroleum, Wanda shi kuma mallakar Nijeriya.

Muna da masaniya an gano danyen man-fetur a garin Oloibiri na Jihar Bayelsa tun a shekara ta 1956, Kamfanin BP, da abokansa irin su Chevron da total da shell da mobil suke cin karansu ba bubbaka.

A shekara ta 1971 ne Nijeriya ta kafa NNOC, wato National Oil Company of Nigeria inda kamfanin ya shiga ƙungiyar massu hako da sayar da man-fetur a Duniya – OPEC, sannan a hankali kuma a shkara ta 2021 ya zama NNPC Ltd. Inda Mele Kolo kyari ya zama Babban Shugaba na dukkan kamfanonin da suke ƙarƙashin NNPC Ltd.

Haka a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida –1985 zuwa 1993 aka samar da ƙungiyar masu sayar da man-fetur da gas da kuma dangogin su ‘yan ƙasa.
Zuwa yau akwai kamfanoni na ‘yan ƙasa masu yang aske suna kasuwancin maan- fetur da gas a faɗin Nijeriya, wasu daga cikinsu sun haɗa da A.Y.M Shafa Limited, Da A.A Rano Nigeria Limited, da BOVAS Limited, Da NIPCO plc, da Rain Oli Limited, da Matrix Energy, da Northwest Petroleum and Gas, da Swift Oil da Nepal Oil and Gas Service limited, da Mainland Oil and Gas Limited da kuma Emadeb Energy, da dai sauransu, kuma su ake bawa tallafi dommin farashi ya dai-daita domin ‘yan ƙasa su samu sa’ida a harkokin rayuwarsu.

Bincike na ƙwaƙwaf a arewacin Na’ijeriya da aka gudanar daga 1960 zuwa 1963 an sami tabbacin samun man-fetur a yankin tafkin chadi dake da makobftaka da Maiduguri da wasu sassa na yankin jihar Bauchi da gwambe da kuma Nassarawa da Kogi .

Amma ciwon hassada da kushe da kuma cin hanci da sashawa na jami’an gwamnatocin baya suke yiwa aikin riƙon sakainar kasha. Allah ya jikan Shugaba Goodluck Jonathan ba don ya mutuba, saboda hoɓɓasa da gwamnatins tayi na waiwayar bincikko sha’anin man-fetur a arewacin Nijeriya.

Wannan hoɓɓasa ta shugaba Jonathan, ta bawa Shugaba Muhammadu Buhari da ya motsa, inda ma’aikatan suke rassa rayuwarsu daga hare-hare na ‘yan Boko Haram. Inda aikin ya tsaya chak sai a wannan shekara ta 2023 Muhamadu Buhari ya sake bada umarni da a cigaba da aiki Bola Ahmad Tunubu ya dora.

Kwatsam, a jawabinsa na rantsuwa Bola Ahmed Tinubu sai ya soke tsarin tallafi. Wanda sabon faifai ne indan Allah ya kai mu mako mai zuwa.

Harkar Man-fetur da Gas a Nijeriya Tun farkon fari ba’a ɗora shi akan ginshikin gaske ba. Kamfanonin da suka fara aiki sune da riba, Ribar Ma da tafi uwar kuɗi, Sukuma yan kasa koo Oho.

Haka Abin yake tafiya Har lokacin Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa. Abin takaici, Bayan Yakin Biyafara da Janar Yakubu gawan ya jagoranta, sai gwamnatin take kukan ta rasa yadda zatayi da kuɗi, hakan tasa aka hambarar da gwamnatinsa.

Gwamnatin Murtala da Obasanjo su suka yi ɓarna da tarihin Najeriya ba zai manta da su ba domin su sukayi Bonas na Odoji da William da dukiyar Nigeria. A wannan Lokaci ‘yan Nigeria suka san darajar kuɗi, aka shiga facaka da siye-siyeh alatu tun
daga kekuna da akwatinan radio da talabijin da na’urorin sanyaya ɗaki da makoshi (Refrigerator)
Aka kuma shiga gine-gine na awan igiya a duk jahohin Nijeriya, daga nan sai hali na gaskiya da amana da taimakon juna suka gushe, kowa ba shi da mutunci sai mai kuɗi. ‘yan fashi da ‘yan daba da kuma ‘yan ɗaukar amarya suka bullo.

Haka kuma fitsara da rashin ta’ido suka zama adon mata, mace mai kunya da kamun kai ta zama baƙauyiya, wacce bata wayeba. Nma da kiwo da muka gada kaka da kakkanni aka yimusu sakainar kashi, kullum sai zance marar kan gado.

Ilimi da yakamata a bashi muhimmanci sai aka ɗora shi a neman kuɗi, wato ilimi a takarda ba ilimi a aiki ba, kowa ya iya turanci wato ya iya magana da Baturan Amurka da Birtaniya, Idan yazo Nijeriya zai iya magana da shugabannida za’a gayyace Biranan Turai da Amuruka, Paris, Berlin, Lisbon, Madrid, Washington DC da kuma Ottawa da ke Canada Domin Kallon Gine-gine da titian da kuma fararan mata suna ta ɗaukar hotuna.

Ga shi mun koro zance, amma lokaci ya cim mana don haka za mu tsaya sai mako mai zuwa, a biyo mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *