Makamashi: Hada-hadar man fetur kan kawo gurɓatar muhalli da yanayi

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Buƙatar a rayu cikin wannan duniya mai cike da ridani, amma cikin sauki da kuma wadata tare da walwala da nishaɗi babu bata lokaci, wato dai rayuwa da suke kira fa ‘Aljannar Duniya; inda za su ci duniyar su da tsinke. Wannan gurɓataccen tunani ya sanya dan Adam harkilo dare da rana ta amfani da kyautar da Allah Subuhanahu wata ala ya ba shi daga Basira da Hikima wadanda yake iya amfani da su wajan sarrafa duk wata halitta mai rai da marasa raiharda makamashi da muke batun sa.

Makamashin farko da Malam Bahaushe ya waye da shi kamar shekaru dari biyar da suka shude, wanda yake fafutukar tara shi a duk farkon shigowar kaka, bayan an girbe amfanin gona, an kai gida sai kuma jama’u su shiga daji don debo Makamashin wuta wanda ake kira ‘Karmo’, Wannan Karmo ya kunshi itacen Yakuwa, da na Itacen Lalle, da na Itacen Kuɓewa, da Itacen auduga da kuma itacen tafasa. Makamashi na biyu shi ake kira da ‘Kara zube’.

Bayan an gama girbe Dawa, akan tara karan na Dawa a yi bishiyar kara da shi a kowace gona. Duk wanda mai gona bai yi bishiya da shi ba, shi yara ‘yan makaranta suke kira “Kara zube,” suke tattarowa su kawo gida a matsayin makamashi, da shi mata suke girke-girken su da shi. Su kuwa makera tun a wancan lokaci suna amfani da itacen kirya wajan samar da wutar da zata iya narka duk wani nau’in ƙarfe tun daga Baƙin ƙarfe da Tagulla da Gorar Ruwa har da danyan zinare da Azurfa da kuma sauran ma’adanai da malam Bahaushe ya waye da su.

Zuwan Nassara mulkin Mallaka a wannan nahiya ta Afirka har da wannan kasa ta Nijeriya a ƙarni na shatara zuwa yau, sun gabatar mana da makamashin Kwal (Coal) a garuruwan Enugu da Abakaliki da Nsukka da Lafia da kuma Assaikio inda suke kwasar wannan makamashi sama ‘tonnes’ dubu hamsin a duk shekara. Shi kuwa man Fetur da dangoginsa waɗannan Nassara ‘yan mulkin mallaka suna kwasa tun a shekara ta 1953 suke zukar miliyoyin ganguna (barrels) na danyan man fetur (Crude Oil) a rijiyoyin da suke kauyukan Edop da Okan da Assa da Ofan da Forcados Yokry da Meren da Usari da Ubit da kuma Oso dukkan su a kudu maso kudu na Nijeriya.

Saboda hada-hadar wadannan makasai-kwal da man fetur an lahanta ɗaukacin wadannan mahallai, farko an gurbata ƙasar noma da kiwo inda tsirrai tun daga ciyayi da bishiyu an kashe su ba su ba sauran fitowa har dan Adam ya amfana daga abubuwan da suke samarwa. Hakan kuma sai ya haifar da zaizayar kasa, Saboda haka sauran halittu da ƙwari da kifaye saboda sinadaran da suka hadu da ruwan sama da ruwa mai gudana a koguna da tafkuna duk sai ya kashe su. Masu suna’ar su sun tashi daga aiki, saboda haka sai talauci da fatara sai su aure su.

Iskar gas da ake fitarwa daga ɗaruruwan rijiyoyin man fetur ita kuma wannan gas dake fita sai ta gurbata sararin samaniya inda makaran da suke kare mu daga zafin rana, hakan sai ya kawo sauyin yanayi wanda ya ɗauki miliyoyin shekaru kafin ya sama. Don haka sai a samu kwarar ruwan sama wanda yafi ƙarfin magudanun ruwa da suke yankin, shi masana yanayi ke kira ambaliya (Overflowing) wanda yake haifar da asarar dukiya da rayuka. Wannan ta sa ya samar da ‘yan fafutukar Neja Delta, wato ‘Movement for the Actualization of the saverign state of Bi’afra (MASSOB).

Duk waɗannan fituna sun samo asali daga samuwar wadan nan makamashi- Kwal da man fetur ganin yadda mahallansu suke gurɓacewa saboda hadahadar da take gudana, amma ba tare da kulawa ta kirki ba. Saboda haka samuwar Man fetur a Arewacin Nijeriya ga mai hankali da hangen nesa yana da ra’ayi guda biyu masu sosa zuciya, wato”, gaba kura baya sayaki”, ga farin ciki duniya ta samu, za a cia sha har wasu suyi teba, ga gidaje na alfarma da motocin hawa har ma da dawakin zage saboda yin kilisa da La’asar sakaliya.

Su kuwa talakawa da marasa ƙarfi za su shiga uku domin kuwa za a gurbatamusu mahallansu, ƙasar noma da kiwo zasu lalace saboda hadadar man fetur idan har ba a ɗauki matakan kariya ga afkuwar kwarar dan yar man man fetur. Wannan shi zai haifar da karan cin abinci da kuma rashin aikin yi domin kuwa noma ba zaiyu ba. Kuma tun da babu ciyawa da za a bawa dabbobi kuma ga talauci, sai ya haifar da mace-mace na dabbobin har da sauran halattu.

Matsalar hadahadar man fetur ta fuce gurbatar mahalli da yanayi take gurɓatar tattalin arzikin duniya wanda kuma ya kai ga gurɓatar siyasar duniya har ma da zamantakewa al’umma kuma ya raunana addini a duniya ta koma mutuwa. Maganar kowa yaya zai sami kudi, kuma kudin babu ishi. Yaro da babba kudi, mace da namiji kuɗi hatta kanana yara kudi, wannan tasa matasa suka shiga kashe-kashe domin su karɓi kuɗi.

Bukatar Makamashi ta koma kamar buƙatar abinci da ruwan sha ga mutane. Idan hadahadar man fetur ta kai ga buƙatar iska ga dan Adam da dabbobi da tsintsaye da kuma ƙwari to, wannan shi ake kira ƙarshen duniya, domin kuwa rayuwa zata sauya kuma babu me iya hasashen mai zai faru. Wato babbar matsalar ita ce ta yawaitar matatun man fetur a ƙasashen duniya, kowacce kasa tana hanƙoran kafa wannan matata-‘refinery’.

A Afirka kawai a kwai matatun man fetur sama da 20 a ƙasashe irin su Algeria, Tunisia, Libya, Egypt, Nigeria, Angola, Sudan da kuma Congo. Haka wannan hadahadar ta man fetur ta kaia samar da iskar gas inda a waɗan nan ƙasashe na Afirka kasar Algeria take samar da kashi 63(63%) da nahiyar dake fitarwa, ita ma Ngeria na fitar da kashi 15 (15%), Egypt na fitar da kashi 14 (14%), Libia da Tunisia na fitar da kashi 8 (8%). Mun kawo wannan misalai ne domin muyi nuni da cewa ba zasu zauna lafiya ba, domin kuwa ƙasashen turai suna da bukatar waɗan nan makamashi.

Hadadar Makamashi-kwal (Coal), Man fetur (Oil), Iskar gas (Gas) da kuma makamashin Yuraniyum (Uranium) Makamashi da kasar Niger ta hako kashi 48 (48%), Namibia na hako kusan kashi 40 (40%), ita kuma ƙasar Afirka ta kudu (South Afirka) na hako kashi 12 (12%), hakan ya sa za kaji rigingimu suna ta barkowa a cikin ƙasa domin su waɗannan ƙasashe na turai su sami damar kwasar wannan dukiya cikin sauki, kuma kuna ta faɗace-faɗace kuna karkashe ‘yan uwanku su kuwa suna cin karnikan su babu babbaka.

Wajibi ne ga wadannan kasashe ‘a Afirka da su tashi tsaye kamar yadda suka kira kan su da ‘Afircan Union (AU) su zama Tsintsiya madaurin ki daya, idan ba haka ba kuwa tarihi zai mai-mai ta kansa. Lokacin da mutum, wato ɗan Adam shi ne dukiya haka wadan nan turawa suka rika zabarin ‘yan Afirka suna bautar da su (Slavery). Haka lokacin da Noma da kiwo shi ne dukiya suka mayar da Afirka saniyar tatsa, Afirka ta zama filin samar musu amfanin gona kamar Auduga da Gyada da Kwakwar manja da katako da Ridi da kuma Fatu da kiraga, saboda masana’antun su daga karshe mulkin mallaka ya biyo baya.

Yan zu makamashi shi ne dukiya kuma ƙasashen Afirka da suka rarrabamu guntu-guntu sun samu damar kwasar wannan makamashi na kwal, man fetur da dangoginsa (gas) da Yuraniyum . Sun Kunna fitila wai ita Damokarad’ɗiya. Sun fito da jam’iyu a duk ƙasa inda za a shekara a na hayaniyar zaɓe sun raba kawunanmu wannan baya biyayya da wannan sai tashin hankali da kashe-kashe.

Sun feso wata guba da suka kira cin hanci da rashawa (Correuption and Bribery) Suka hade da waccar gubar Damakaraɗiya (Democracy) domin su kwashi waɗannan makamashi na man fetur da Gas da kwal da kuma Yuraniyum. A biyo mu mako mai zuwa domin aji yadda makamashi ya zama makamin mulkin mallaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *