Makarantar GSS ta yaye ɗalibai 697 a cikin shekara 15

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Makarantar sakandare da firamare ta GSS wato Guidance Standard School da ke Kano ta yaye ɗalibai 697 a cikin shekara 15 da kafuwarta.

Shugabar makarantar Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman FIDA, ita ta bayyana hakan a yayin bikin yaye ɗaliban, inda ta ce ɗalibai 697 a ɓangarori daban-daban na makaranatar a ƙoƙarinta na tallfawa al’umma da ilimi musamman marasa ƙarfi a cikin al’umma wanda makarantar ke ba kamar yadda ta kamata ako wane lokaci, domin bunƙasa ilimi daidai da manufar gwamnatin Kano wajen samar da ilimi mai nagarta ga al’umma.

Kamar dai yadda shugabar makarantar ta yi bayani a wurin taron yaye ɗalibai 69 da raba kyaututuka ga ɗaliban da malamai da sauran al’umma da suka nuna hazaqa, ƙoƙari da tallafawa illimi a wurin biki da aka yi a ranar Asabar da ta gabata a harabar tsohuwar Jami’ar Bayero da ke Kano.

A jawabinsa Sheikh Malam Nasidi Gauron Dotse, ɗaya daga cikin manyan baƙi ya bayyana cewa tsarin koyar da addini da karatun zamani a wannan makaranta ta GSS abu ne mai kyau kuma shi ne ya kamata kowace makaranta ta yi domin taimakon duniya da lahirar ɗan Adam, sai kuma ƙoƙari da kyakyawar niyya, ta shugaban makarantar Barrista Bilkisu Ibrahim Sulaiman kuma Shugabar Ƙungiyar Mata Lauyoyi ta Duniya reshen Jihar Kano, da cewa ta cigaba da jajircewa wajen taimaka wa ilimi da al’umma.

Tun da farko a jawabinta Barista Bilkisu ta ce maƙasudin samar da wannan makarata shi ne amsa kira ga yin alkairi da umarnin Allah Maɗaukakin Sarki na kowa ya zo ya bada gudumawasa ta alkairi.

Kuma illimi da tarbiyya na daga cikin abubuwan alkairi da ya kamata ɗan Adam ya bada gudunmawa, don haka ne su ke ƙoƙarin bada wannan gudunmawa kamar yadda ta kamata, kuma abun godiya ga Alah shi ne yadda al’umma ta ke amfana da wannan makaranta inda kuma ta yi kira ga ɗaukacin shugabanni makarantu, manya da ƙanana da ka da su manta da koyarwa, amana ce kuma aiki ne mai daraja don haka su guji duk wani abu da zai gurvata tarbiyya musamman kaɗa-kaɗe da duk wani abu da ya saɓa al’adar mu da addinimu, inji shi.