Makinde ya sake buɗe kasuwar Shasha

Daga AISHA ASAS

Bayan shafe kimanin makonni biyu da rufe kasuwar Shasha a jihar Oyo sakamakon ɓarkewar rikici a tsakanin ‘yan kasuwan kasuwar, Gwamna Seyi Makinde ya bada umarnin sake buɗe kasuwar ba tare da wani jinkiri ba.

Makinde ya buƙaci sake buɗe kasuwar ne yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin Hausawa da Yarabawan yankin a fadar gwamnatin jihar da ke Ibadan.

Gwamnan ya ce an ɗauki matakin sake buɗe kasuwar ne duba da yadda rufe kasuwar ya yi tasiri kan tattalin arzikin yankin da ma jihar baki ɗaya.

Ya ce yayin da ya ziyarci Sarkin Sasa da Baale ya fahimci jama’a a takure suke da batun rufe kasuwar, saboda an rufe inda suke samu suna gudanar da harkokinsu.

Ya ci gaba da cewa, idan aka dubi jihar Oyo, ko a lokacin da cutar korona ke ganiyarta bai rufe kasuwa ba saboda sanin cewa mutane da dama sai sun fita kasuwa kafin su samu abin kaiwa bakin salati da iyalansu.