Makomar Arewa ta fi ƙarfin siyasar 2023

Daga ISAH ABDULLAHI ƊANƘANE

A Arewa lokaci ne a yanzu da ake buƙatar haɗin kai, ajiye bambancin ra’ayin ni ɗan Jam’iyyar APC ko PDP ko APGA ne ko dai wacece don haɗin kai, a samu nasara

Lokaci ya yi da ‘yan Arewa za su dawo su yi wa kansu karatun ta natsu, a ajiye ƙiyayya, hassada, kwaɗayi da tsoro tsakanin juna, a fuskanci babbar barazana da ke barazana ga ƙara raba makomar Arewa, da suka haɗa da: rashin ingantaccen tsaro, talauci, yunwa da rashin ayyukan yi, da kuma matsalar taɓarɓarewar ilmi.

Dattawan Arewa da masu riƙe da madafun iko da ake ganin su ne sitiyarin samar da ci gaba ko makoma ga ‘yan Arewa suna da ƙalubalen da ke gabansu, na gaya wa junansu gaskiya a kan sun kasa riɓe amanar da magabata irin su Sardauna, suka bar musu a kan makomar ‘yan Arewa da Nijeriya bakiɗaya.

Lokaci ya yi da za a zauna a yi wa juna gafara a haɗa kai don ganin an ceto ‘yan ƙasa dake fuskantar ƙalubalen tashin hankali na kisan gilla, hare-haren cin amana da ƙone dukiya da ake yi a Arewa ba gaira ba dalili.

Zancen makomar Arewa a 2023 ba shi ne abin bayar da fiffiko ba. Muhimmin abu shi ne, fuskantar waɗannan ƙalubalen dake da mummunar illa ga rayuwar al’ummar Arewa, musamman a yankin Arewa maso Yamma inda noma ya zama tashin hankali ga jama’a.

Sai shugabani sun zauna tare, su amince a zuciyoyinsu za su sanya tsoron Allah su yafe wa juna, su ajiye hassada da kwaɗayin mulki da son rai, sa’ilin za a iya samun nasara ga lamarin da zai taimaka a kawo sauƙi ga waɗannan matsalolin.

Akwai hatsari mai yawa wasu ‘yan ƙalilan don sun ga suna da wata mafita har su yi ko oho ga bayar da haɗin kai a fuskanci wannan barazana.

Muddin wasu ko wani ke ganin, idan babu shi Arewa ba za ta cimma wannan burin ba, tabbata wannan matsalar ba za ta kai warshe da sauqi ba.

Duk ɗan Arewa yana da haƙƙi ga ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yankin. Don haka, lokaci ya yi da za a ajiye ra’ayin siyasa, a manta da ƙabilanci na harshe ko addini a dawo ga gina ƙasa a samar wa jama’a kwanciyar hankali.

Isah Abdullahi Ɗanƙane, matashi ne ɗan gwagwarmayar kare haƙƙoƙin al’umma, da ke zaune a garin Gusau na Jihar Zamfara. 0704 081 8166