Malam Shekarau: Baƙin ka ja, ake fassara maka

Daga AMINU ƊAN-ALMAJIRI

Har kullum ya kamata mutane su dinga waiwayar tarihi domin idan wani abun ya faru su, zama masu alƙalanci na gaskiya. 

Dukkan abinda kuka ga yana faruwa da Malam Ibrahim Shekarau yau a siyasa, shi ne ya rubuta littafin hakan da kansa ake fassara masa, bisa dalilai kamar haka:

A shekarar 2003, Malam Ibrahim Shekarau ya shiga jama’iyyar ANPP. A wancan lokacin ba shi ne ɗan takara ba, Aminu Little ne ɗan takararsu. Haka aka canja aka bashi, bashi din da aka yi adalci kenan ko dai-dai ne? 

Bayan ya kammala wa’adin mulkinsa, sai aka zo batun tsai da magajinsa, a lokacin ga su mataimakinsa, su Kabiru Gaya da sauransu duk suna buƙata, sannan su ne kusan waɗanda suka dace su gaje shi, amma haka ya ɗauko Takai ya bashi, saboda shi ne muradinsa basu ba. Hakan ɗin dai-dai ne ko adalci?

 A 2019, ya shigo APC bayan fitar sa daga PDP, ya shigo a dai-dai lokacin an fara hada-hadar  tunkarar zaɓe, an tsayar da ɗan takarar Sanata a wannan lokacin, amma haka aka ƙwace aka bashi, shi yafi kowa sanin ba abinda ya yi na cancanta aka ɗauka aka bashi. Na farko, me ya sa bai yi batun makomar yaransa na siyasa a wannan lokacin ba? Sannan da ya karɓi kujerar takarar sanata, dai-dai ya yi ko adalci? 

Idan muka dawo ɓangaren saɓanin sa da NNPP, yanzu saboda Allah ka zo ka samu mutane sun sha wahalar gina gidansu, babu sisin ka balle kwabonka a wannan wahalar. Sun ga kana ta rara-gefe a hanya suka janyo ka, suka dawo da kai inuwa domin ka huta. Lokaci ɗaya saboda tsabar zaƙewa, ka ce kaso 70% na gidan naka ne? 

Jama’a, saboda Allah mu yi aiki da hankali. Idan Kwankwaso ya bawa shekarau abinda yake buƙata, shi wace riba ya samu a duk wahalar da ya yi kenan? 

Sannan tunda shi shekarau yana kukan kwankwaso ya yaudare shi, me ya sa tun farko bamu ji shi da yaran sa sun faɗa wa Duniya cewa, ga yarjejeniyar da aka yi ba sai yanzu? Me ya sa tun da baya tunanin makomar yaransa idan buƙatarsa ta biya sai yanzu da yaga za su yi masa bore?

Idan har ta tabbata duka jama’iyyun da ya dinga canza sheƙa daga 2003 zuwa yanzu 2022 zalintarsa suke, me ya sa ba zai kafa tasa jama’iyyar shi da jama’arsa su wayata ba, kamar yanda Kwankwaso, malam ibrahim khalil, Sha’aban Sharaɗa suka yi ba? Waɗannan amsoshin kawai nake buƙata. Sai kun sake jina jama’a.

Aminu Ɗan-Almajiri ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga jihar Kano.