Malaman Addini a Kano sun amince da takarar Tinubu a 2023

A yau daya daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai ci a yanzu ya halarci daurin auren, yar babban jami’in tsaron shugaba Muhammadu Buhari a Kano. Bayan kammala wannan daurin aure da aka yi a masallacin Alfurqan, dake unguwar Nasarawa GRA, Mista Tinubu ya halarci wani taro da aka shirya na musamman da gamayyar manyan malaman jihar.

A wannan taro dai, Malaman sun nuna goyon bayansu ga takarar jagoran na APC, ta bakin daya daga cikinsu, Shehi Shehu Maihula.

“Muna sane da rawar da ka taka wurin zaben daya daga cikinmu, wanda a baya ya sha gwagwarmayar neman zama shugaban kasa bai samu ba, har sai da ka dafa masa, da yardar Allah, sannan ya samu ya kai gaci. A dan haka, mu ma za mu nuna maka halacci, mu saka maka da irin alherin da kayi mana” in ji Shehi Shehu Maihula na dariqar Tijjaniyya.

Tun da farko da yake amsa tambaya daga manema labarai, ya bayyana cewa, shi ba siyasa ce ta kawo shi Kano ba, ya zo ne domin halartar daurin auren a gidan abokinsa, dan haka ba abinda ya gama wannan ziyara ta sa da siyasa.

Jagoran dai ya samu rakiyar tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu, da kuma Mista Bisi Akande,  kuma gwamna AbdulLahi Umar Ganduje na jihar Kano ne da kan sa ya raka Jagaban zuwa daurin auren da kuma wurin taron. Tuni dai Mista Tinubu ya koma garin Kaduna, inda ake sa ran zai kaiwa, mai martaba sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ziyarar ban girma a goben.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*