Malaman Kano sun nesanta kansu da batun tsige Sheikh Ibrahim Khalil daga muƙaminsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Zauren Haɗin Kan Malamai da Ƙungiyoyin Musulunci na Jihar Kano ya nesanta kansa da wata sanarwa da ya ce wasu mutane sun bayar game da sauke Sheikh Ibrahim Khalil daga matsayin shugabancin Majalisar Malamai ta Ƙasa reshen jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha’awar ya shugabance ta.

Jagororin wannan zaure sun ce sam wannan mataki ba da yawunsu aka zartar da shi ba.

Sanarwar da jagororin zauren suka fitar wadda ta sami sa hannun sakataren zauren, Dr. Saidu Ahmad Dukawa, kuma mai ɗauke da kwanan wata 12 ga Oktoba, ta ce, “Jagorancin Zauren Haɗin Kan Malamai da Ƙungiyoyin Musulunci na Jihar Kano sun samu labarin wata sanarwa da waɗansu mutane suka bayar suna masu iƙirarin sauke Sheik Ibrahim Khalil daga shugabancin Majalisar Malamai ta Ƙasa reshen jihar Kano, tare da ayyana wanda suke sha’awar ya shugabance ta.

“Jagororin suna masu tabbatar wa al’umma cewa ba da yawunsu aka yi wannan jawabi ba kuma ba sa goyon bayansa.

“Harkullum jagororin suna neman zaman lafiya ne da haɗin kan arumma, amman wannan yunƙurin zal haifar da saɓanin haka ne.

“Don haka Zaure yana kira ga alumma da su ci gaba da ririta zaman lafiyar Kano su guji duk wani abu da zai iya zama barazana ga tsaro da kwanciyar hankali.

“Jagororin da suka amince da a fitar da
wannan sanarwa su ne kamar haka:

  1. Farfesa Musa Muhammad Borodo
  2. Khalifa Sheik Ƙaribullah Sheik Nasiru Kabara
  3. Sheik Abdulwahhab Abdallah
  4. Sheik Ibrahim Shehu Maihula
  5. Farfesa Muhammad Babangida Muhammad
  6. Dr, Bashir Aliyu Umar
  7. Imam Nasir Muhammad Adam
  8. Dr. Ibrahim Mu’azam Maibushira.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *