Man City ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City ta lallasa Real Madrid mai riƙe da kambun gasar Zakarun Turai a wasan daf da na ƙarshe, nasarar da ta bai wa jagorar Firimiyar damar kai wa wasan ƙarshe na gasar inda za ta haɗu da Inter Milan a Istanbul.

An dai ta shi wasan na ranar Laraba ƙwallaye 4 da nema wanda ke nuna huce haushin City kan tawagar ta Carlo Ancelotti da ta fitar da ita daga gasar sau 2 a irin wannan mataki, kuma a jumulla Manchester City ta yi nasara da ƙwallaye 5 da 1 idan haɗa da haɗuwar ta da Real Madrid a wasan farko.

Yayin wasan na ranar Laraba dai Bernado Silva ne ya zama ɗan wasa mafi hazaƙa bayan ƙwallayensa biyu a minti na 23 da kuma minti na 37 da suka baiwa City gagarumin rinjaye tun a zagayen farko na wasan.

Duk da cewa Coutois ya yi nasarar tare ƙwallaye 2 da Haaland ya nufaci zurawa tun a zagaye na farko amma wannan rashin nasarar ta jiya ta zama wasa mafi muni da Madrid ta yi a baya-bayan nan ƙarƙashin gasar ta cin kofin Zakarun Turai.

Kamar dai yadda wasan farko ya gudana kowanne vangare ya kange ’yan wasan gaba na abokiyar karawarsa da ake fargabar su iya zura ƙwallo, ta yadda aka gaza ganin tasirin ’yan wasan irinsa Haaland da De Bruyne ko da ya ke ya taimaka wajen zura ƙwallaye 2 haka zalika Karim Benzema da Vinicius Junior har ma da Rodrygo da suka gaza kataɓus.

Manchester City wadda ke shirin dage kofin Firimiya da zarar ta yi nasara a haɗuwarta da Chelsea ranar Lahadin nan ta na kuma tunkarar wasan ƙarshe na cin kofin FA da za ta haɗu da Manchester United a wasan ƙarshe, wannan na nuna cewa ta na tunkarar kofuna 3 a cikin wannan kaka.

A ranar 10 ga watan Yuni ne dai za a doka wasan ƙarshe tsakanin Cityn wadda ba ta taɓa lashe kofin gasar ba da kuma Inter Milan da ta lashe kofin sau 3 wato a shekarun 1964 da 1965 da kuma 2010 wanda ya zama lokaci na ƙarshe da ta kai matakin wasan ƙarshe, wato shekaru 13 da suka gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *