Daya daga wanda ya yi haɗakar mallakar Manchester United, Sir Jim Ratcliffe na duba yiwuyar yadda za a ƙara rage ma’aikatan ƙungiyar.
Wata majiya ta tabbar da cewar Man United na duba yadda za ta kara rage kuɗin da take kashewa da zai kai yuro miliyan 300 a shekara uku.
Man United ba ta ce komai ba kan rahoton cewar Ineos Group, ƙarƙashin Ratcliffe na auna yadda zai sake rage ma’aikata kimanin 100 zuwa 200 ba.
Daga baya ne za a fayyace yawan ma’aikatan da za a rage da guraben da suke aiki, domin aiwatar da shirin.
Haka kuma United za ta rufe ofishinta da ke Landan a Kensington, amma ta sanar cewar za ta ci gaba da kasancewa a cikin birnin don hulɗar kasuwa.
Tun farko United ta rage ma’aikata 250 da cire butum butumin Sir Aleɗ Ferguson a matakin jakadan da ake biya da soke biyan kuɗi ga ma’aikata, domin zuwa kallon wasan ƙarshe.
Man United ta ce za ta yi amfani da kuɗin da za ta samu daga rage ma’aikatan, wajen bunƙasa babbar ƙungiyar da sauran ayyuka.
ƙungiyar ta Old Trafford ta ce kuɗin da za ta samu zai kai yuro miliyan 45m a kowacce shekara daga rage ma’aikatan.
Haka kuma wani babban jami’in ƙungiyar da ya dade kan mukamin kula da gudanar da Man United, Jackie Kay wanda yake Old Trafford shekara 30 zai ajiye aikin.
Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai yuro 300 a Man United, domin bunƙasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa.
Ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe yuro biliyan 2, ko kuma a yi wa Old Trafford kwaskwarima da zai ci yuro biliyan 1.5.
United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai yuro miliyan 113.2 daga ranar 30 ga watan Yunin 2024.
Man United tana ta 13 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24.