Managartan matakan kawar da talauci a Xinjiang sun amfanawa al’ummar yankin matuƙa

Daga MINA

Abokai, a wannan mako “duniya a zanen MINA” yana bayani ne kan yadda wani manomi a yankin Xinjiang mai suna Halik Geym ya fita daga kangin talauci da samun ƙarin arziki.

Wannan ɗaya ne daga cikin manyan na’urorinsa na aikin noma masu inganci da yake amfani da su wajen shuka amfanin gona iri daban-daban.

A shekarar 2021, kuɗin shigarsa ya kai kuɗin Sin Yuan miliyan 1.8 (kwatankwacin dalar Amurka dubu 260).

Amma yau wasu shekarun da suka gabata, ya sha fama da talauci, bai iya samun amfani gona da yawa ba, saboda garinsa na dab da hamada, ba sa samun ruwan sama sosai kuma yanayi ba shi da kyau.

Saboda irin waɗannan matsalolin da al’ummar ke fuskanta, ya sa ƙasar Sin ta ɗauki matakin da ya dace don ba su taimako, Halik Geym ya sami rancen kuɗi, inda ya sayi injinsa na farko.

Ban da haka kuma, a shekarar 2020, rukunin aiki a garinsa ya gayyato wani masanin kimiyya zuwa wurinsu, don koyar da manoma dake wurin fasahar shuka amfanin gona.

Amfanin gona da Halik Geym ya samu, ba ma kawai ya biya dukkan rancen kuɗi da ake binsa ba, har ma ya sayi ƙarin injunan noma.

Managartan manufofin da Sin ta ɗauka, sun bai wa manoma damar koyon fasaha da kimiyya na zamani, abin da ya kyautata zaman rayuwarsu da samun ƙarin arziki.

Halik Geym ya ce, zai kafa ƙungiyar haɗin kai ta masu amfani da injunan aikin gona da ƙungiyar kula da harkokin ’ya’yan itatuwa da kansa, don yayata abubuwan da ya koya, ta yadda sauran manoma za su iya samun arziki tare.

Mai zane, kana marubuciya: MINA