Maniyyata su shirya, akwai aikin Hajji bana, inji NAHCON

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamishinan tsare-tsare, bincike, ƙididdiga da kuma yaɗa labarai na hukumar aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Mamoh, ya bayyana cewa, bana ’yan Nijeriya za su samu damar sauke farali a ƙasa mai tsarki.

Prince Mamoh ya bayyyana cewa, babu tantama suna da tabbacin wannan shekarar 2022, maniyyata za su gudanar da aikin Hajji.

Da yake fira da manema labarai, kwamishinan ya yi kira ga maniyyata da ke faxin Nijeriya su fara shiri tun yanzu.

Haka zalika, Kwamishinan, wanda ke jagorantar ɓangaren tsare-tsare, ya ƙara da cewa, hukumarsu na shirin kawo sauyi domin sauƙaƙa abubuwa a aikin Hajji.

A cewarsa, tun bayan dakatar da aikin Hajji saboda ɓarkewar annobar Korona, NAHCON ta ci gaba da aiki ba dare ba rana domin ƙara inganta aikin Hajji ta yadda ’yan Nijeriya za su samu sauƙi.