Manoman Ƙasar Sin sun hudanar da bikin girbi na bana

Daga CMG HAUSA

Miliyoyin manoma a ƙasar Sin, sun gudanar da bikin girbin amfanin gona na bana a Juma’ar nan, bikin irin sa na 5 da aka ƙirƙira domin murnar samun yabanya mai yalwa.

A bana ma an gudanar da bikin a sassan ƙasar Sin daban daban, yayin da ake hasashen samun amfanin gona mai yawan gaske, duk da bazuwar annobar COVID-19, da tsananin zafi da aka fuskanta a shekarar.

Bayan haye ƙalubalen ambaliyar ruwa da aka samu gabanin shiga hunturu a shekarar bara a yankin arewacin ƙasar, da lattin shuka alkamar hunturu, da sake bazuwar annobar COVID-19, da tsanantar yanayin zafi da fari a wasu sassan kudancin ƙasar, an samu karuwar hatsi da aka noma a yayin bazara, da shinkafa ‘yar wuri a wannan kaka ta bana.

An fara gudanar da bikin girbin amfanin gona na ƙasar Sin ne a shekarar 2018, yana gudana kuma a daidai lokacin da tsayin sa’o’in rana ke yin daidai da na dare, ɗaya daga cikin lokuta mafiya muhimmanci 24, a kalandar noma ta gargajiyar Sin, ya kan kuma fado ne duk shekarar tsakanin ranekun 22 da 24 ga watan Satumba, a lokacin da ake tsaka da girbin amfanin gona.

Mai fassara: Saminu Alhassan