Manufar Amurka game da yankin tekun Indiya da Pasifik ba za ta yi nasara ba

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya, taron majalisar ministocin ƙasar Nepal, ya yanke shawarar dakatar da haɗa gwiwa tare da ƙasar Amurka, kan wani shirin da ake kira SPP, ko kuma shirin dangantakar abokantaka tsakanin jihohi.

Kafafen yaɗa labaran ƙasar Nepal sun ruwaito cewa, tun a shekara ta 2015, sau da yawa Amurka ta bukaci Nepal ta shiga shirin SPP, amma Nepal din ba ta yarda ba, saboda damuwar ta kan ƙulla ƙawancen soja da Amurka.

Daftarin shirin SPP tsakanin Nepal da Amurka, na ƙunshe da abubuwa da yawa, ciki har da ƙaddamar da atisayen soja a yankin filato na Nepal, sa’annan rundunar tsaro ta Amurka, za ta iya shiga cikin Nepal ba tare da wani tsaiko ba, kana, Amurka za ta samar da bayanan sirri na yaki da ta’addanci, da na’urorin aikin soja ga Nepal da sauransu.

Abun lura a nan shi ne, duk waɗannan abubuwa na da alaka da aikin soja, kana, tamkar shisshigi ne cikin harkokin cikin gidan Nepal.

Ƙasar Nepal na bakin iyaka da kasashen Sin da Indiya, inda a ‘yan shekarun nan, kasar Amurka take kara aiwatar da manufarta game da yankin tekun Indiya da Pasifik, a wani yunƙuri na shigar da Nepal a ciki.

Haƙiƙanin gaskiya, irin abun da Amurka ta yi a Nepal, shi ne yunkurin shawo kan ƙasar Sin. Kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya yi jawabin cewa, ya kamata a “gina” muhalli bisa manyan tsare-tsare a kewayen ƙasar Sin. Maƙasudin ɓangaren Amurka a zahiri shi ne, kawo cikas ga ci gaban ƙasar Sin. Amma irin abun da Nepal ta yi a wannan karo, yana kawo tsaiko ga manufar Amurka, kana hakan masomi ne kawai.

Ko shakka babu, manufar Amurka game da yankin tekun Indiya da Pasifik da take ƙoƙarin yayatawa, ba za ta yi nasara ba.

Fassarawar Murtala Zhang