Manufar Gidauniyar Hausa da Haɗa kan Hausawan Duniya shi ne martaba kimar Bahaushe – Dr Saidu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban Gidauniyar haɗa kan Hausa da Hausawan Duniya, Dakta Sa’idu Muhammad Ghana ya bayyana cewa kusan shekaru huɗu da kafata tana cigaba da samun karɓuwa sosai a tsakanin Hausawa a faɗin duniya.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a Kano ya ce sun assasa gidauniyar ne da kyakkyawan manufa ta haɗa kan al’ummar Hausawa a duniya duk inda Bahaushe ya samu kansa ya zama ana taimakawa juna da ƙulla dangantaka da kyautata rayuwa.

Ya ce “akwai sosa rai matuqa idan ka je wasu ƙasashen sai ka ga yara ƙanana masu jin Hausa suna barace-barace koda ba Hausawa ba ne ana kallonsu a Jausawa da samun haɗin kai a tsakanin Hausawa a duniya za a iya kawo gyara.”

Dakta Sa’adu ya ce sun soma assasa gidauniyar ne daga dandalin yanar sadarwa wanda yanzu aƙalla suna da mambobi sama da 600,000 a duniya gaba ɗaya kama daga Nahiyar Afirka da ƙasashen Turawa da na Larabawa har ma da wanda suke Amurka da Kanada da yankunan Chana.

Ya ce ita Gidauniyar Hausa da haɗa kan Hausawan Duniya a ƙasar Ghana aka soma kafata ta yaɗu a yammacin Afirka da sauran ƙasashen duniya baki ɗaya.

Ya ce yanzu gidauniyar cibiyarta a Nijeriya take domin shi a matsayinsa na shugaban ta Bahaushe ne shi ɗan ƙasar Ghana kuma akwai ‘yan Benin, Kamaru, Sudan da suke da asali da Hausawan Arewacin Nijeriya sai suka ƙiƙiri gidauniyar suka ga dacewar a yi mata cibiya a Nijeriya.

Dakta Sa’id Muhammad ya ce tun kafa gidauniyar ba su taɓa haɗuwa gaba da gaba sun yi taro ba sai dai ta yanar sadarwa amma yanzu akwai tsare-tsare da suke na gudanar da taronsu na duniya a jihar Kano a matsayinta ta cibiyar Hausa.

Ya ce suna da kyautatawan alaƙa da iyayen ƙasa sarakuna da malamai shi ya sa a farkon shigowarsa Nijeriya ya kai ziyara masarautar Kano ya gabatar da kai da manufarsu ta gidauniyar haka ma ya ziyarci masarautar Daura da Sarkin Zazzau duk ya gabatar musu da gidauniyar sannan yana shirin zuwa fadar Sarkin musulmi da na Katsina da sauran sarakunan Arewa.

Dakta Sa’id Muhammad ya ce: “Sarkin Kano da na Daura da sauran sarakuna da suka ziyarta sun karɓe su hannu biyu. Kuma su da suke ƙasashen duniya suna kallon yadda rashin haɗin kai na Hausawa ke jawo musu muzantawa amma cikin ƙasar nan balle su da suke a waje shi ya sa suka ga kamatar a haɗa kai a riƙa magana da yawu ɗaya da maganta matsaloli.”

Dakta Sa’id Muhammad ya koka da cewa a zuwansa ƙasar nan ya samu kule daga wasu ‘yan Nijeriya da suke cewa wai ya ya ɗan Ghana zai zo ya riƙa magana akan Bahaushe. Kuma suna da take na gidauniyar na “Mu Kauda Bambanci mu yaƙi jahilci kada mu zubar da mutuncinmu”.

Don haka duk wanda ka ga ya soma kawo bambanci to yana da qarancin sani domin yau Hausa ya fi ƙarfin ƙasar Hausawa kawai domin za ka sami hausawa a ɗimbi a kowane lungu da saƙo a Duniya amma abinda ke damun hausawa shine bambance- bambace.”

Shugaban gidauniyar na Hausa da haɗin kan Hausawa na duniya, Dakta Sa’id Muhammad ya yi kira ga al’umma musamman na jihar Kano su zo a haɗa kai a kauda cin zarafin da cewa ai kai kaza ne ko daga kaza kake ko kai ba Bahaushe ba ne duk ba zai kai ba.

Mu haɗa kai tamkar sauran ƙabilu da suke magana da harshe ɗaya a duniya amma mu Hausawa mun samu rauni don haka wannan gidauniyar tana ƙoƙarin samun nasarar ganin Hausawa a matsayin abu ɗaya a duk duniya.