Manufar Sin ta faɗaɗa buɗe ƙofa ga waje za ta tallafawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

Daga SAMINU ALHASSAN

Masharhanta da dama sun nazarci muhimman batutuwa da aka tattaunawa, yayin babban taron wakilan JKS na 20 da ya kammala a kwanan nan, tare da yabawa alƙawuran da shugaba Xi Jinping na ƙasar Sin ya ambata, cikin jawabinsa yayin ganawa da ’yan jaridu, lokacin kammalar taron na bana, musamman ma gabar da ya ambato aniyar ƙasar sa, ta kara fadada buɗe ƙofarta ga ƙasashen waje, tare da tabbatar da nasarar manufar zurfafa gyare-gyare a dukkanin fannoni, da samar da ci gaba mai nagarta.

Har ma ya sha alwashin cewa, Sin za ta samar da ƙarin damammaki ga duniya.

Ko shakka babu, idan aka yi duba da irin gudummawa da ƙasar Sin ke bayarwa ga bunƙasar tattalin arzikin duniya, haɗi da yadda a yanzu shugabannin take ƙara tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da yin tafiya kafaɗa da kafaɗa da sauran sassan duniya, za a amince da cewa, ci gabanta zai ƙara faɗaɗa ci gaban duniya baki ɗaya.

A matsayinta na ƙasa ta 2 mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, Sin na da kasuwa mai yalwa, wadda ke ƙara jan hankulan duniya. Don haka ne ma masana ke ganin wannan manufa, ta ƙara buɗe ƙofa ga sassan duniya da Sin ta alƙawarta, za ta tallafawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya, tare da amfanar da al’ummun ƙasa da ƙasa.

Kawo yanzu, Sin ta zamo babbar abokiyar cinikayyar ƙasashe sama da 100, ta kuma kafa yankunan cinikayya maras shinge, tare da sanya hannu kan muhimman yarjeniyoyin cinikayya, irinsu cikakkiyar yarjejeniyar haɗin gwiwar raya tattalin arziki ko RCEP, da dandalin raya haɗin gwiwar Sin da nahiyar Afirka na FOCAC da sauransu.

Bugu da ƙari, Sin na taimakawa ƙasashe masu tasowa da musayar fasahohi, yayin da ayyukan da ake gudanarwa ƙarƙashin shawarar ziri daya da hanya daya, suka buɗe sabon babi ga raya cuɗanyar cin moriyar juna, tsakanin ta sasssan duniya daban daban.

Mai fassara: Saminu Hassan