Manufarmu ce tsamo matasa daga ƙangin talauci da aikata laifuffuka – Kwamaret Alkamatu

Kamfanin Alkamatu Kamfani ne da ya yi fice a jahar Kano, wajen samar wa da al’umma mafita don dogaro da kai. Sannan suna samar wa da mutane bashi daga bankuna tare da tallafin kuɗaɗe don cigaba da kasuwanci don tsayawa da ƙafafunsu. Wakilin Blueprint Manhaja a Kano, Babangida S. Gora ya samu tattaunawa da Shugaban Kamfanin Alkamawa. Ga yadda tattaunawar ta kasance. 

MANHAJA: Da farko za mu so mu ji da wa muke tare.

ALKAMATU: Ni Sunana Alkamatu Hussaini Abdulƙadir, Kuma ni ne shugaban wannan kamfani na Alkamatu BrainBox Solutions.

Mene ne manufarka ta samar da wannan kamfani?

to kusan kasan yanzu mafi yawancin matsaloli na rashin aikin yi ya yawaita. Idan ka yi duba ga matasa a yanzu za ka ga da yawan laifuffuka dake faruwa matasa ne aka fi samu a cikinsa. To tare da karyewar Tattalin arziki a ƙasar nan da rashin aikin yi, wannan ne ya farkar da ni wajen tunanin yadda za mu ciro wannan matasa daga wancan ƙangi da aka fi samunsu ciki na laifi ta hanyar samar masu hanyar dogaro da kai wajen bashi ko  taimako daga ɓangarorin dake ba da tallafi don yadda sama musu mafita  tare da rage laifufuka.

Tsahon wanne lokaci kuka fara wannan tafiya?

To yanzu dai zan iya cewa, kusan shekaru biyar kenan da farawa. Don tun shekarar 2017, ka ga shekara biyar kenan da kafuwar wannan kamfani namu.

Daga lokacin da kuka fara wannan aiki naku na ciro al’umma daga ƙangi da matsin rayuwa wanne ƙalubale kuke fuskanta?

Magana ta gaskiya duk abinda ka ɗauko don cimma wani buri na rayuwa ko kuma sauya da yawan mutane daga abinda kake ganin marar kyau ne zuwa hanya mai ɓullewa. Ko kuma canza su daga wani tunani zuwa wanda ya fi shi kyau, to lallai akwai ƙalubale mai tarin yawa da za ka iya tunkara. Haka kuma, ita kanta gwamnatin dake mulki idan za ka yi irin waɗannan abubuwan ba ka cike ƙa’idojin da take buqata ba, to za ta iya dakatar da kai ko akasin haka. To lallai mun yi qoqari wajen cike duk wani abinda ake buƙata don ganin mun tallafa wa al’ummarmu wajen sana’a don rage wa gwamnati aikin da ya kamata ta yi.

Ya kake kallon jihar Kano a fuskar kasuwanci?

Ya zuwa yanzu dai za mu iya cewa, jahar Kano ta yi shuhra wajen kasuwanci. Don Allah ya albarkaci garin nan da albarkarsa a ƙasar nan da ma maƙwabtan Nijeriya. Don haka, muke ƙoƙarin ganin mun tallafa wa al’ummar jahar kano wajen ganin ta zama cibiyar kasuwanci a Afirka bakiɗaya.

Akwai rahotanni daga bakin shugaban banki Tony Elumelu da suka bayyana cewa, qungiyarku ta ba da jari kyauta ga mutane 133. Me za ka ce game da wannan rahoto?

Magana ta gaskiya na ji daɗi sosai musamman ta yadda muka yi kira ga jama’ar jahar Kano wajen zuwa ga abinda muke nufi. Kuma cikin yardar Allah aka amsa kiran mu, inda wannan ƙungiya ta samar wa da ‘yan kasuwar jahar abinda ba a taɓa ba na jari har kimanin naira milyan 300, Kuma kyauta ba tare da tunanin yadda za ka maida ba ko kuma yadda za ka ɗora wani abu yayin maida kuɗin ba. Sannan kuma koda gwamnati za ta ba da kuɗi haka, ba lallai ta iya fidda kuɗi haka zuwa kai tsaye ga waɗanda ake so su samu  kai tsaye ba.

Dole sai an samu wata tangarɗa. Lallai na ji daxi matuƙa, don kodayaushe ba abu ne mai kyau ba a ce duk lokacin da ka samu kuɗi ko wata dama ka zama kai kaɗai za ka amfana da ita ba. Ya kamata ka buɗa kowa ya samu wannan tagomashin, don a samu sauƙi a rayuwa. Tare da fitar da mutane daga ƙangin babu da ya yi yawa ahalin yanzu, ya zamana ka tallafa wa wanda yake buƙatar a taimaka masa. Kamar yadda muka samu daga wannan gidauniya ta Tony Elumelu, mu ma mun  faɗaɗa. Wanda ba abin alfahari ba, yanzu mutane da dama sun samu gudunmuwa tare da hanyar dogaro da kai bakin gwargwado. An fidda jama’a da yawa daga talauci tare da sama masu jari da aka yi ta nan fannin.

Za ka iya faɗa mana adadin yawan mutanen da wannan gidauniyar ta sama wa hanyar dogaro da kai, kama daga ba da jari ko rance ko kuma koyar da sana’a?

A yanzu dai muna da mutane sama da dubu uku da suka samu horo da tallafi daga garemu. Kuma bakin gwargwado idan mun horas da mutane mukan bibiyi abinda muka ɗora su a kai don tabbatar da haƙiƙanin abinda aka ɗora su a kai; Sun maida hankali ko kuwa akasin haka? Don ka san wai an ce: “za ka iya tasa keyar godiya zuwa rafi, amma kuma ba za ka iya tilasta mata ba ta sha ruwa, har sai idan tana da buƙatar shansa”. Ma’ana a nan ita ce, za ka ga ka koyar da mutane sana’a da basu jari, kuma sun karɓa tare da aikatawa. Amma daga ƙarshe idan ba ka bibiyarsu, sai ka ga abin bai yi ƙarko ba. Ko kuma sun yi amfani da kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.

Ko akwai wani shiri da wannan kamfani na Alkamatu yake yi don ganin ya faɗaɗa wannan shiri nasa a sauran jihohin Arewacin Nijeriya?

Eh to, duba da yadda jahar Kano take matakin gaba wajen kasuwanci ya sa muka fi maida hankali kacokan ga ita Kano a yanzu. Amma Kuma idan dama ta bada, yanzu muna shirya-shiryen ƙara faɗaɗawa zuwa sauran jahohi kamar Jigawa da Katsina. Amma kasancewar matsalar tsaro mun ɗan dakata har sai mun ga an samu sauƙin matsalolin dake faruwa a yankunan. Don kuwa wannan zai ƙara tallafawa da qara bunƙasa tattalin arzikin jahar da taimaka wa matasa ta fuskoki daban-daban.

Waɗanna matsaloli kuka fi fuskanta a wannan tafiya?

Farko dai muna godiya ga Allah wanda ya ba mu nasarori da suka shafe wacannan matsaloli. Amma mafi yawan matsalar da muka fi fuskanta su ne yadda gwamnati take wa al’umma alƙawurra da dama amma kuma daga ƙarshe, ta kasa cikawa. Don mun sha cike takardu da dama wajen ganin an taimaki jama’a, kuma gwamnatin take saka mu. Daga karshe sai a samu matsala ta kasa cika wannan alƙawarin. Dan haka, da yawa sai mun yi ƙoƙarin fahimtar da al’umma yadda abin yake, tare da nuna musu abin sai an bi a hankali. To ita ma wannan gwamnati ya kamata ta yi ƙoƙari wajen fahimtar muna rage mata aiki ta wannan fuskar.

Sannan kuma ba zai yiwu ba a ce sai mun bi wasu ƙungiyoyi na ƙasa da na waje dan nemoma al’umma hanyar dogaro da kai wajen ganin an gudu tare, an tsira kuma tare. Don haka, mu a nan muna ganin rashin goyon bayan gwamnati gare mu shi ne babban ƙalubalen da muka fi fuskanta. Su ma al’umma sukan bamu matsala inda za ka ga kai ka taimaki mutum, maimakon ya qara maida hankali wajen ya taimaki wasu, amma kuma sai mutum ya ƙi.

Mene ne kira ko buƙatarku ga gwamnati?

Ba mu da buƙatar da ta wuce gwamnati ta shigo a yi tafiyar nan da ita, tare da su ma masu hannu da shuni. Haka kuma su ma wanda suka amfana da irin wannan tallafi da su taimaki wasu su ma ɗan rage talauci da rashin aikin yi a jahar Kano. Duk da cewa ba ‘yan jahar Kano kaɗai suka amfana da wannan tallafi ba akwai sauran jahohi kamar Katsina da Jigawa. Don haka, su ma su ƙoƙarta wajen ganin sun taimaki wasu yadda abin zai zagaya.

Wanne kira za ka yi wa al’umma a kan su mayar da hankali su nemi na kansu?

Tabbas dukkanin Wanda za mu iya ba wa shawara bai wuce cewa lallai ka da ka raina sana’a ba. Don akwai Alkhairi cikinta. Ko fiyayyen halitta da sauran manzanni da ubangiji yake turowa, to babu wanda bai yi sana’a cikinsu ba. Kuma ma ita ce abinda suke samun rufin asiri acikinta. Don haka, ba a raina sana’a, komai ƙanƙantarta mutum ya riƙe ta da ƙima da kuma maida hankali.

Meye saƙonka na ƙarshe ga sauran al’umma?

Farko, Ina godiya ga Allah da ya ba mu rai da lafiya da kuma dama kasancewa a wannan ƙadami. Sai godiya maras misaltuwa ga iyayena da suka tarbiyyantar da ni da ɗaukar nauyina bakin gwargwadon iyawarsu, har zuwa yanzu. Sai malamaina da suka koyar da ni ilimin da nake alfahari da shi a yanzu. Akwai abokan aikina da muke aiki ba dare, ba rana wajen ganin mun yi nasara da jajircewarsu da ƙoƙarinsu don ni kaɗai ba zan iya aiwatar da wannan aiki ba sai da taimakonsu. Akwai masu bani shawarwari har muka kai ga samun nasara, kuma har yanzu suna ƙara taimakawa wajen shawarwari, ina godiya matuƙa.

Dangane da waɗanda suke ganin sun nema ba su samu ba, me za ka ce game da batunsu?

To, ka san kowa dakake gani. Ya kamata mutane su fahimci samu da rashi. Kuma duk abinda Allah ya baka ikon samu, to daga gare shi ne. Kuma akasin haka ma, daga gare shi ne. Don haka, ko ni ma sanda na nemi wannan tallafi daga gidauniyar Tony Elumelu na farko ban dace ba. Amma kuma na biyu, na samu, kuma ga shi mun samar wa al’ummar jihar kano abinda Allah ya ƙadarta. Dan haka, kowa ya sa wa ransa da lokaci ya yi, to babu makawa ko menene Allah zai tabbatar maka da shi matuƙar ka tsaya ga Allah mai badawa. Don haka, mu a shirye muke wajen ganin an taimaki jama’a da shawarwari da tallafi da ma bashin da za su inganta kasuwancinsu. Buƙatarmu a nan ita ce, kowa ya samu dai ya yi amfani da shi ta hanyar da ya dace.

Mun gode da lokacin da ka ba mu.

Mu ma muna godiya bisa wannan dama da ba kowa ke samun irinta ba.