Daga SANI AHMAD a Abuja
Ɗan takarar gwamna a Jam’iyar PDP a Jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido ya ce yana da manufar inganta tattalin arzikin Jihar Jigawa a cikin shekara 35 masu zuwa idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna.
Mustapha, wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan jihar Sule Lamido, ya ce dole ne su zauna da masu ruwa da tsaki a jihar domin tabbatar da wannan burin nasa idan har ya zama gwamnan.
“Za mu haɗa kai da ƙwararru da sarakuna da malamai wajen samar da aiki ga matasa.
“Muna so mu ɗora Jigawa akan tafarkin inganta ta a cikin shekara 35 domin ta tsaya da ƙafafunta a fagen tattalin arziki,” inji shi.
Baya ga wannan kuma ya shaida wa BBC cewa batun samar wa matasa aiki abu ne da ya tsaya masa a rai.
Ya kuma ce zai yi ƙoƙarin ganin matasa sun samu abun yi ta hanyar bunƙasa masana’antu da kuma kafa wasu a jihar.