Manufofin taimakawa al’ummar Xinjiang guda tara

DAGA MINA

Abokai, gwamnatin kasar Sin ta taba gabatar da manufofin taimakawa al’ummar Xinjiang guda 9. Yau “duniya a zanen MINA” zai gabatar muku yadda Sin ta aiwatar da daya daga cikin wadannan manufofi, wato manufar taimakawa al’ummar Xinjiang wajen samun aikin yi, matakin da ya inganta zaman rayuwar al’ummar yankin.

Matar dake cikin wannan zane sunanta Jimilanmu Makmuti, wadda ma’aikaciya ce a wata masana’antar samar da kayayyaki dake Xinjiang, ta ce: “na samu aiki mai kyau, zan samu zaman rayuwa mai kyau nan gaba”.

A shekaru 4 da suka gabata, Jimilanmu Makmuti da iyalanta sun dogara ga dan albashin da mijinta ya samu. A shekarar 2018, hukumar kauyenta ta samar mata aikin yi a kusa da gidanta, hakan ya sa ta iya samun kudin shiga tare da kula da iyalinta. Yanzu, Jimilanmu Makmuti tana samun kudin shigar da ya kai yuan RMB 2500 a ko wane wata, matakin da ya kyautata zaman rayuwar iyalanta, har bi da bi ne ta sayi mota da sauran na’urorin jin dadin rayuwar yau da kullum a gidanta.

Kyautatuwar zaman rayuwar Jimilanmu Makmuti, wani misali ne na amfanin wannan manufa.

A ‘yan shekarun nan, jihar Xinjiang na kokarin tabbatar da wannan manufa, inda garuruwa da kauyuka 1173 sun kafa hukumomin ba da tabbacin zaman rayuwar al’umma. Ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan mutanen da suka samu aikin yi ya kai miliiyan 13.6, wanda ya karu da mutane miliyan 1.14 bisa na shekarar 2012.

Guraben aikin yi na da muhimmanci ga iyalai, kana hanya daya tilo ta samun kudin shiga. Wannan manufa na taimakawa al’umma samun aikin yi, da kyautata zaman rayuwar al’umma.

Hakika al’ummar Xinjiang na amfana da wannan manufa sosai, wadda ta kai su ga samun zaman rayuwa mai cike da alheri da kwanciyar hankali.

Mai zane kuma rubuta: MINA