Manyan jami’an PDP bakwai sun ajiye muƙamansu saboda rashin adalci

Wasu manyan jami’an jam’iyyar PDP a matakin ƙasa su bakwai sun ajiye muƙamansu daga Majalisar Zartarwa ta Ƙasa ta jam’iyyar.

Waɗanda lamarin ya shafa su ne, Mataimakin Sakatare na Ƙasa, Diran Odeyemi; Mataimakin Mai ba da Shwara Kan Sha’anin Shari’a na Ƙasa, Ahmed Bello; Mataimakiyar Shugaban Mata ta Ƙasa, Umoru Hadizat; Mataimakiyar Jami’in Bincike na Ƙasa, Divine Amina Arong; Mataimakin Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa, Hassan Yakubu; da kuma Mataimakin Sakataren Kuɗi na Ƙasa, Irona Alphonsus.

Baki ɗaya jami’an sun danganta ajiye muƙaman nasu da rashin shugabanci nagari da adalci daga ɓangaren Shugaban PDP na Ƙasa, Prince Uche Secondus.

Ɗaya daga cikin jami’an wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana irin rashin kulawar da sugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Secondus ke nuna musu tun bayan da aka zaɓe su a 2017.

A cewarsa, “Tun bayan da aka zaɓe mu a 2017 sau uku kacal muka gana da Secondus. A haka ɗin ma ba wai shi ne ya buƙaci ganin mu ba, mu ne buka buƙaci hakan.

“A gare shi ba mu da wani amfani. Alhali kowannenmu na da mazaɓarsa da kuma mabiya. Da alama ba su ɗauke mu komai ba face wani nauyi da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ɗora musu,” in ji shi.

Sakataren Hulɗa da Jama’a na PDP na Ƙasa, Mr Kola Ologbondiyan, ya tabbatar da jami’an sun ajiye muƙamansu inda ya ce, Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa na jami’yyar ya samu wasiƙunsu na ajiye muƙaman nasu.

Ologbondiyan ya ce shugabancin jami’yyar zai dubi lamarin kana ya ɗauki matakin da ya dace kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *