Marafa ya ƙaryata komawarsu PDP

Daga BASHIR ISAH

Sanata Kabiru Marafa ya ƙaryata rahoton da ke nuni shi da tohon gwamnan Zamafara, Abdulaziz Yari sun sauya sheƙa sun koma jam’iyyar hamayya ta PDP.

A rana Lahadi aka jiyo shugaban PDP na jihar Zamfara na cewa sun cimma jarjeniniya tare da waxanda lamarin ya shafa tare da cewa nan bada daxewa ba za su bayyana komawarsu PDP a hukumance.

A kan haka ne Sanata Marafa ya ce, “Abin da muka sani shi ne muna kan tattaunawa da jam’iyyun siyasa da dama wadanda suka buqaci mu shigo cikinsu a jihar.”

Cikin zantarwar da ya yi da kafar Tambarin Hausa a Zamfara, Marafa ya ce, “….a yanzu dai duk wani lbarin da ya nuna mun sauya sheƙa zuwa PDP, ƙarya ne. Kuma har yanzu ba mu cimma matsaya da kowannensu ba.

“Ba gaskiya ba ne cewa mun koma PDP. Don haka nake kira ga jama’a da su yi fatali da duk wani labari da ke nuni da hakan har sai sun ji daga gare mu….”

Sai dai Sanata Marafa ya ce barin su APC ya ya zama wajibi sakamakon irin rashin adalcin da aka nuna musu, “Ba mu da zaɓin da ya wuce ficewa da daga APC,” in ji shi.

Ya ce sabon shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, bai kira shi ba. “Abdulaziz Yari dai ya faɗa mini cewa Abdullahi Adamu ya neme shi sun tattauna, kuma an sanar da ni matsayin tattaunar da suka yi.

“…Ya shaida mini cewa zai yi tafiya, don haka yana so in wakilce shi lokacin tattaunar, amma ya zuwa yanzu babu wanda ya tuntuɓe ni,” in ji Marafa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *