Marigayi Momoh: “Dattijo mai dattako, mai kishin ƙasa, ɗan jarida abin koyi” – inji Tinubu

Daga UMAR M. GOMBE

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Chief Bola Tinubu, ya bayyana marigayi Tony Momoh a matsayin “Dattijo mai dattako, mai kishin ƙasa kuma ɗan jarida abin koyi.”

A saƙon ta’aziyya da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan sha’anin labarai, Mr Tunde Rahman, Tinubu ya bayyana alhininsa dangane da mutuwar Tony Momoh.

Yana mai cewa, “Na tuna wata tattaunawar da aka yi da shi da na karanta a ɗaya daga cikin jaridun ƙasar nan a ‘yan kwanakin da suka gabata, inda ya bayyana irin son da yake yi wa ƙasarsa da kuma fatansa a gaba.

“Ya kasance mutun mai kishin ƙasa wanda ke son haɗin kai da cigaban ƙasa.”

Jigon ya ci gaba da cewa, marigayi Momoh ya samu sanayya a gida da waje a lokacin da yake riƙe da muƙamin editan tsohuwar jaridar Daily Times.

Haka nan ya ce, “Momoh ba ɗan jarida ba ne kawai don kuwa a fagen siyasa ba a bar shi baya ba. Hasali ma da shi aka kafa jam’iyyar APC, sannan ya kasance na kusa da Shugaba Buhari.”

Kazalika, Tinubu ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga ƙasa. Daga nan, ya miƙa ta’aziyarsa ga iyalan marigayin, tare da fatan Allah Ya ba su dangana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *