Martabar aikin jarida da ƙalubalen da manema labarai ke fuskanta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba da jimawa ba ne aka gudanar da bukin ranar kare mutuncin ’yan jarida daga tsangwama da cin zarafi ta duniya, da nufin faɗakar da jama’a, musamman hukumomi da jami’an tsaro, muhimmancin tsare haƙƙoƙin ɗan jarida da masu neman labarai, da mutunta su. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware kowacce ranar 2ga watan Nuwamba na kowacce shekara ta zama ranar da za a rika haɗuwa ana tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar manema labarai a fagen samar da bayanai.

Duk da irin rawar ganin da ’yan jarida ke takawa a fagen wayar da kan jama’a game da al’amuran dake faruwa a ƙasashen su da sauran ɓangarorin duniya, har yanzu ana cigaba da samun rahotannin kisa, ɗauri, ko cin zarafi da ƙuntata yanayin tsarin tafiyar da aiki, a sassa daban-daban na duniya. Wata ƙungiya mai rajin kare haƙƙoƙin ‘yan jarida ta ‘Protect Journalists’ ita ma ta fitar da rahoton cewa, ’yan jarida da dama ne ke kulle a gidajen yari daban-daban na ƙasashen duniya.

Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar da wani rahoto da ke bayyana cewa, a duk bayan kwana 4 ana kashe ɗan jarida ɗaya, a tsawon shekaru goma da suka gabata, musamman a ƙasashen da ake fama da ƙalubalen tsaro da yaƙe-yaƙe, Rahotanni sun bayyana cewa a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2020 an kashe ’yan jarida kimanin dubu 12, a yayin da suke gudanar da aikin su na neman rahotanni.

Gwagwarmayar da ’yan jarida ke sha wajen sadaukar da lokacin su da rayuwarsu don ganin sun samar da muhimman bayanan da za su taimakawa al’umma, ta hanyar faɗakar da su da wayar musu da kai game da yadda za su inganta rayuwar su, ba ƙarama ba ce, amma kuma abin takaicin shi ne ƙalilan ne daga cikin al’umma suke yabawa da wannan ƙoƙarin na su. A wajen hukumomi kuwa ai ba su da waɗanda suke kallo a matsayin riƙe-wuya ko barazana, kamar ’yan jarida.

Tun a shekarar 1972 da wata jaridar ƙasar Amurka ta Washington Post ta fara bankaɗo abin fallasar nan na Watergate, wanda ya jawo murabus ɗin shugaba Richard Nixon, ’yan jarida suka zama abin tsoro a wajen ‘yan siyasa da masu mulki.

‘Yan jarida da dama a ƙasashen duniya daban-daban sun taimaka wajen kawo canje-canje masu ma’ana ta hanyar rubuce-rubuce ko shirye-shiryen da ake watsawa ta kafofin watsa labaran su, irin su matashin mai gabatar da shirin talabijin ɗin nan na ƙasar Rasha, Edward Sagalaev, wanda a ƙarshen shekarun tamanina (1980s) ya kawo canji a siyasar ƙasar, wajen shirya muhawara da tattaunawa game da batutuwan da suka shafi makomar ƙasar, a ƙarƙashin shugabancin Gorbachev na wancan lokacin.

A nan Nijeriya ma rayuwar ‘yan jarida da mutuncin aikin su na cigaba da fuskantar barazana iri-iri, daga waɗanda ke kallon aikin nasu na yin karan-tsaye ga mulkin su ko manufofin su na siyasa. Kuma hakan na jawo ‘yan jarida da dama suka samu kansu a wani mawuyacin hali da ya haɗa har da kisa.

Na san ba za ku manta da batun zargin da aka yi wa tsohuwar gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Babangida a shekarar 1986 ba, dangane da kisan gillar da aka yi wa tsohon editan mujallar Newswatch, Dele Giwa ta hanyar aika masa wasiƙa mai ƙunshe da bom, kwanaki biyu bayan jami’an tsaron farin kaya na SSS sun yi masa wasu tambayoyi.

Ba a ƙarƙashin gwamnatin mulkin soja ba hatta a wannan mulkin na Dimukraɗiyyya ma ‘yan jarida na ganin tasku iri-iri daga hannun jami’an tsaro da shugabanni da ke zargin ‘yan jarida da hassala wutar rikice-rikicen ƙabilanci da siyasa wanda yanzu haka ƙasar nan ke fuskanta, ko kuma batun ɓata sunan gwamnati a idon talakawan ƙasa.

Ba za mu manta da wani abin takaici da ya faru wa na batun tsare wasu ‘yan jarida huɗu da ke aiki da kamfanin Leadership Newspapers, a lokacin mulki tsohuwar gwamnatin shugaba Jonathan, don sun ƙi su bayyana haƙiƙanin inda suka samo wani labari da jaridar ta buga da ke zargin tsohon shugaban da ƙoƙarin ganin shirin da wasu jam’iyyun adawa ke yi na haɗewa waje ɗaya bai samu nasara ba.

Ban manta da abin da ya faru a shekarun baya ba, da mataimakin editan jaridar Al-Mizan da wani wakilin jaridar game da wani rahoto da jaridar ta buga na cin zarafin jama’a da jami’an rundunar tsaron haɗin gwiwa na JTF ke yi a garin Potiskum na Jihar Yobe ba, inda aka tsare su har fiye da mako guda, kuma aka muzgunawa iyalansu, duk da sunan yin bincike da tabbatar da tsaro.

Har kawo lokacin da nake wannan rubutu ɗan jarida Okechukwu Nnodim da ke aiki tare da jaridar PUNCH yana hannun masu garkuwa da mutane da ke neman kuɗin fansa har Naira Miliyan 10 kafin su sake shi. Bayan ya shafe tsawon watanni 8 a hannun ’yan ta’adda. A Nijeriya da wasu ƙasashen da ke cikin fitinar ta’addanci irin wannan rayuwa ce ’yan jarida ke fuskanta, bayan ƙunci da tsananin da suke rayuwa a ciki na rashin kyan albashi da rashin muhallin da ya dace na gudanar da aiki.

Wannan hali da ‘yan jaridar Nijeriya da wasu ƙasashe masu tasowa, ke fuskanta ya sa Majalisar Ɗinkin Duniya da gwamnatin ƙasar Amurka ke tsawatar wa gwamnatoci da kwamandojin yaƙi a fagagen fama daban-daban, game da buƙatar sakar wa ’yan jarida mara su gudanar da aikin su cikin ‘yanci da aminci!

Yayin da muke ƙara jinjina da yabawa ga irin rawar ganin da ‘yan jarida ke takawa, muna kuma fatan ganin canje-canje na cigaban aikin jarida, da ya haɗa da inganta muhallin aiki, da kyautata albashi da sauransu.