Martabar aikin jarida da ƙalubalensa a yau

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wata muhawara ta tashi a makon da ya gabata dangane da wani batu da ya harzuƙa wasu ‘yan jarida na Arewa, sakamakon yadda shirin wasan kwaikwayo na talabijin mai dogon zango na LABARINA zango na 3 fitowa ta goma sha ɗaya, ya nuna yadda aka bai wa wani ɗan jarida abin hasafi don ya yi kuɗin mota, bayan wata hira da ya yi da wani a cikin shirin.

Wannan fita da aka nuna ta hassala mutane da dama, musamman ‘yan jarida, da suka riƙa bayyana mabambantan ra’ayoyi kan dacewa ko rashin dacewar abin da aka nuna ta yadda wasu ke ganin zubar da mutuncin aikin jarida ne, wanda kuma aka riqa ɗora laifin abin a kan daraktan shirin Malam Aminu Saira. Duk da kyakkyawan zaton da jama’a ke yi masa na nuna ƙwarewa cikin finafinan da yake ba da umurni.

Duk da kasancewar ba kasafai nake samun zarafin zama na bibiyi shiri mai dogon zango a kowacce fitowa ba, amma na samu damar kallon wannan shirin da ake taƙaddama a kai, kuma nima akwai wasu abubuwa da ban ji daɗin yadda aka gabatar da su ba. Ko da yake ba za a yi zargin da gangan ba ne, sai dai a ce ajizanci ne na aiki.

Na karanta wasu ra’ayoyi da hirarraki da aka yi da wasu manema labarai game da wannan al’amari da ya tava zuciyar ‘yan jarida, kuma na fahimci ƙorafinsu, wanda ba wai ya tsaya kan masu shirya fim ɗin LABARINA ba ne kawai, har ma da yadda wasu ‘yan siyasa, jami’an tsaro, da wasu ‘yan Nijeriya suke nuna wa wajen yi wa ‘yan jarida kallon ƙasƙanci, rashin mutunci, ko maroƙa. Abin da yake matuqar ci wa ‘yan jarida tuwo a ƙwarya.

Wani ɗan jarida da ya nemi a sakaya sunan sa ya bayyana takaicinsa na yadda a cewar sa daraktan fim ɗin ya nuna martaba da ƙarfin tasirin da waƙa take da shi wajen isar da saƙo, kamar yadda jarumar shirin Sumayya ta yi amfani da basirar ta wajen shirya waƙar da ta ja hankalin tsohon saurayinta Mahmud ya koma gidan iyayensa, amma a lokaci guda kuma sai aka shigo da ɗan jarida da ke neman ƙarin bayani game da sabuwar waƙar da aka fitar. Amma Naziru Sarkin Waƙa a matsayin sa na ubangidan Sumayya a shirin, ya qi yarda ya amsa tambayoyin da aka yi masa, sai ma cewa da ya yi a nemi kuɗin mota a ba shi. Shi kuma ɗan jarida cikin sanyin jiki ya sa hannu ya karɓi tukwicin da aka ba shi a ƙasƙance kamar almajiri!.

Wannan shi ya harzuƙa mutane da dama da suka kalli shirin, waɗanda ke ganin Darakta Malam Aminu Saira wulaƙanta aikin jarida ya yi a wannan fitowar, amma kuma yana ɗaukaka harkar waƙe-waƙe, kuma yana martaba ta. Duk kuwa da kasancewar aikin jarida, wasan kwaikwayo da waƙoƙi ɓangarori ne masu kamanceceniya da juna ta fuskar isar da saƙonni ga jama’a da kuma wayar da kan ‘yan ƙasa.

Baban Kyauta, wani ɗan jarida ne mai zaman kansa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ya bayyana takaicinsa na yadda ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati ke kashe maqudan kuɗaɗe wajen ɗaukar nauyin mawaƙa da masu shirya finafinai, amma ‘yan jarida da ke aikin yaɗa saƙonnin ayyukan da suke yi, ba a san da zaman su ba, babu wani tallafi da suke samu daga ‘yan siyasa, ko wata kwangila mai tsoka da za a iya damƙa musu su gudanar don samun amfani. Hakan ke nuna irin fifikon da ake bai wa mawaƙa hatta a gwamnatance, su kuma ‘yan jarida ko oho.

Wani fitaccen ɗan jarida, mai kamfanin jaridar yanar gizo ta ‘Daily Nigerian’ Ja’afar Ja’afar a wani tsokaci da ya rubuta game da batun ya yi nuni da cewa, abin da aka nuna a fim ɗin LABARINA ba laifi ba ne, sai dai sun fito da haƙiƙanin ƙalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta ne, na rashin samun albashi mai kyau, rashin mutuntawa da rayuwar hannu baka hannu ƙwarya da yake ciki.

Shi kuwa abokin aikinsa da ke tare da kamfanin jaridar yanar gizo ta ‘Premium Times’ mai suna Abdul’Aziz Abdul’Aziz nuni ya yi da cewa, ba za a ce masu fim ɗin LABARINA sun ci zarafin aikin jarida ba kai tsaye, idan aka yi la’akari da irin yadda wasu ‘yan jarida ke ba da dama ana wulaqanta su da ɗaukar su a ƙasƙance, saboda yadda suke sa rai da karɓar na goro daga wajen waɗanda suka yi wa aiki.

Ko da yake a cewar sa, na san maganar bai wa ɗan jarida kuɗi tana kuma da nasaba da al’ada. Yawanci babba yana ganin abin kunya ne na ƙasa da shi ya haɗu da shi bai bashi komai ba. Don haka bai wa ɗan jarida (wanda yawanci yaro ne matashi) “kuxin mota” ya zama kamar karramawa ce irin ta al’ada, misalin irin wannan shi ne al’adar bada na goro ga ma’aikatan gidan abinci (restaurants) musamman a ƙasar Amurka. Su abin kunya ne ma ka ci abinci ba ka ƙara wani abu ba akan kuxin abincin, domin kyautatawa ga ma’aikata. Da na tambaya a wata tafiya da na yi Amurka sai aka ce min suna saka “tip” ne saboda yawanci ma’aikatan ba a biyansu da kyau, don haka abinda suka haxa a hannun kwastoma da shi suke ƙarawa a kan albashinsu.

Ya qara da cewa, sai dai kuma a ɗaya hannun kamar yadda ma’aikacin gidan abinci a Amurka ba ya samun kyakkyawan biya, haka ma yawancin ma’aikatan jarida a Nijeriya, ga kuma buƙatun rayuwa na yau da kullum.

Ba baƙon abu ba ne a ƙasar nan a bai wa ɗan jarida na goro ko abin hasafi, don yabawa da ƙoƙarinsa, ko ƙarfafa masa gwiwa don ya ji daɗin gudanar da aikinsa yadda ya kamata. Ko da yake, hakan laifi ne sosai a ƙa’idar aikin jarida, amma saboda halin da ‘yan jarida suka samu kansu a ciki a ƙasar nan ya sa hakan ya zama kamar al’ada. A wani wajen ma har ciniki a ke yi kan abin da ya dace a bayar, wani lokaci in ba a bayar da wani abu ba ma ana iya ajiye labari.

Ɗan jarida Abdul’Aziz yana daga cikin masu takaicin halin da ‘yan jarida suka samu kansu a ciki a ƙasar nan, inda yake cewa, ‘masu kafafen yaɗa labarai da dama basu damu da sauke haƙƙin ma’aikatansu a kansu ba. Gidajen jarida da dama basa biyan albashi, ko kuma suna biyan abinda ko sati guda ba zai ishi mutum ba. Wasu kamfanonin da suka san muhimmancin kula da ma’aikata domin yin aikin yadda ya kamata suna ƙoƙari sosai.’

Wannan yana ƙara nuna mana cewa, tun tashin farko aikin jarida shi ne yake zaman tamkar turke na huɗu na ginshiƙan dimukraɗiyya, sakamakon kusancin sa da jama’a da Gwamnati. Shi ne tsanin da talakawa ke takawa su isa ga shugabannin su, wakilan su na siyasa da isar da koke koken su ga waɗanda abin ya shafa. Don haka ne ma mutunta ɗan jarida da girmama shi yake da matuƙar muhimmanci ga al’ummar da ta san ciwon kanta. Amma mu a ƙasar nan babu maƙasƙanci kamar ɗan jarida, ba a sanin darajar sa sai ana a cimma wata manufa wacce sai da shi za a kai ga nasara. Duk cikar taro da girman sa sai da ɗan jarida yake tasiri, ya zama kamar gishiri a cikin miya. Amma hakan bai amfanar da shi da komai ba, don ko abinci ne a wajen taro, sai a raba da kowa, amma a manta da na gefen ‘yan jarida. Bai fi ƙarfin jami’an tsaro su wulaƙanta shi ko muzanta shi a cikin taro ba, saboda yadda yake masa kallon rashin daraja.

Ko da yake, an ce in ana ta varawo a yi ta mai kaya. Mu kan mu ‘yan jarida muna da wasu halaye da bai kamata a samu a tare da mu ba. An ce ɗan kuka shi yake jawowa uwarsa jifa, kuma lallai idan an zo irin wannan batun tilas a faɗa. Wasu daga cikin mu ba sa sanin darajar kansu, kuma ba su damu da kiyaye dokokin aikin ba, matuƙar za su samu kuɗi. Musamman a wannan lokaci da kowa ke ganin zai iya zama ɗan jarida, saboda yana da babbar waya a hannun sa ko ya iya rubutu, sai kawai ya yi wa aikin shigar burtu, babu qwarewa da sanin ƙa’idojin aiki, yana bayyana kansa a matsayin ɗan jarida. Ganin haka ya sa wasu ke yi mana kuɗin goro suna mana ganin kamar duk haka muke. Kaico!

Duk wanda ya kare mutuncinsa a aikin jarida, yana zaune zai ga alherin aikin yana zuwa masa, kamar yadda Ja’afar Ja’afar ya faɗa. Matuƙar muna son jama’a su ci gaba da ganin kimar mu da martabar mu to, mu kawar da kai daga duk wani abin hannun su. Mu tsaya mu yi aiki tsakani da Allah, ba tare da nuna kwaɗayi ko son zuciya ba. Kamar yadda ya zo a hadisi, manzon Allah mai tsira da aminci yana cewa, ka guji abin hannun mutane, sai mutane su so ka.

Shawara ta ga masu shirya finafinai, kamar yadda suka sani, ita ce su riƙa faɗaɗa bincike a duk lokacin da suke son yin wani shiri da ya shafi wata sana’a ko aiki, tare da sanya jaruman da suka dace su fitar da saƙon da ake son isarwa ta hanyar wasan kwaikwayo. Ba ma faɗa da masu shirya fim, domin ‘yan uwan mu ne kuma abokan aiki, saboda akasarin mu marubuta ne da ke rubuta fim ko labarun da suke zama ƙashin bayan shirya finafinai.

Mu ƙaddara abin da ya faru a shirin LABARINA kuskuren fahimta ce daga su har mu. Amma, don Allah a riƙa yin hattara ana girmamawa da kiyaye mutuncin juna.

Allah ya taimake mu baki ɗaya.