Martabar sarakunan gargajiya da ƙalubalen tsaro

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka gudanar da taron tunawa da Marigayi Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato a wani gagarumin taro da aka gudanar a birnin Kano, ƙarƙashin jagorancin Gidauniyar Tunawa Da Sardauna, wanda aka yi wa taken ‘Farfaɗo da Masarautun Gargajiya Don Inganta Tsaro Da Zaman Lafiya A Arewa’.

Wannan babban taro ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Gwamnonin Arewa, ministoci, ’yan majalisu, sarakuna, malamai, malaman jami’o’i da sauran su. An kuma gabatar da jawabai masu kama hankali sosai, dangane da makomar sarautun gargajiya da muhimmancin su ga harkokin samar da tsaro da zaman lafiya.

Wannan ba ita ce tattaunawa ta farko ba da aka tava yi dangane da batun muhimmancin sarakuna da tasirin su a cikin al’umma. Ba ni kaɗai ba, da dama manazarta da masu nazarin al’amuran yau da kullum sun yi ta bayyana buƙatar muhimmancin samar wa sarakunan gargajiya matsayi na musamman a kundin tsarin mulkin ƙasa.

Abin takaici ne sosai yadda aka mayar da rawanin sarakunan mu na gargajiya, iyayen ƙasa ya zama abin wulaƙanta da cin mutunci. Masarautun da ke da ɗimbin tarihi na addini da na adalci, wanda suke da ƙarfin faɗa a ji da tasiri a wajen talakawan su, an mayar da rawunan su abin ƙasƙantarwa.

A duk lokacin da wasu marasa kunya ko tsagera daga cikin al’umma suka ga an yi wani abu da ya savawa son zuciyarsu. Sai ka ga an samu wasu da za su riƙa ambatar sunan su ko a fakaice suna faɗar maganganu marasa daɗi da ba su cancanta ana gaya wa sarakuna masu martaba ba. Babu ma kamar idan ya shafi siyasa ko mulki, misalin abin da ya faru a Jihar Kano lokacin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, sakamakon tsanantar da rikicin sa da Gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi. Ko kuma a lokacin mulkin soja da aka cire tsohon Sarkin Gwandu Marigayi Mustapha Jakwalo, da kuma tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki.

Dubi dai tunzurin da ya faru a lokacin zaven tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa ’Yar’adua lokacin da aka riƙa kai wa fadojin manyan sarakunan Arewa da gidajen su hari, saboda zargin da aka yi na tsoma bakin su a siyasar lokacin. Haka a yankin kudu maso kudancin ƙasar nan, an samu rahotannin irin yadda ’yan tsagera a yankin suka riƙa zuwa fadojin sarakunan yankin su, suna zane sarakunan su da bulala, kamar wasu yara ’yan makaranta.

A baya bayan nan ma lokacin zanga zangar EndSars, an ga yadda tsageran masu zanga-zanga suka afkawa fadar babban basaraken Jihar Legas suka yi kaca-kaca da ita, suka wulaƙanta muhimman kayan tarihi na gidan sarautar Oba, wanda wasu ba za su taɓa dawo wa ba.

Idan kun tuna haka wasu ɓata gari suka sace mai martaba Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Atto Bunguɗu, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna shi da direban sa, haka aka riƙe su har tsawon kimanin wata guda. Babu irin wulaƙanci da azabtarwar da ba su masa ba.

Ban da wannan babban basarake, akwai wasu fadoji a sassan ƙasar nan da aka afka musu ko aka kai musu hari da sace sarakunan da ke ciki. Kamar misalin abin da ya faru a fadar babban basaraken ƙasar Mushere a qaramar hukumar Vokkos da ke Jihar Filato, inda wasu ɓata gari suka je har gidan sa suka sace Sarkin Mushere, kuma mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Chibi Dariye.

Matsalolin tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, da Arewa maso Yamma, sun kori wasu sarakuna daga fadojin su, sakamakon yadda ake ci gaba da haifar da asarar rayuka da dukiyoyin talakawansu.

Wasu rahotanni da suka riƙa fitowa daga jihohin Zamfara da Sakkwato, inda ɗan ta’addan daji Bello Turji da jama’arsa suke aikata ɓarna da cin zarafin jama’a, an ce har sarakuna suke saukewa da naɗa waɗanda suke so, a yankunan da suke da ƙarfin iko, abin da ya jefa rayuwar sarakunan da iyalan su cikin matsala sosai.

Ko da yake, a wasu wuraren sarakunan gargajiya na kuskure sosai wajen shiga siyasa, da sarayar da ’yancin talakawan su saboda son zuciya, ba tare da haɗa baki da wasu masu hali ana yi wa talakawan su ƙwacen filayen noma, ƙwacen dabbobi, har da ƙwacen matan wasu ko lalata da wasu mata daga cikin talakawan su. Waɗannan na daga cikin dalilan da ke tunzura talakawa kan sarakunan su, har su yi masu wani abu na rashin kunya ko rashin kyautatawa.

Alal-haƙiƙa, halin da sarakunan mu na gargajiya suke ciki a wasu sassan abin tausayi ne da takaici. An bar su da tuma tuman rawani amma babu ƙarfin iko ko wani aiki na musamman da suke gudanarwa a hukumance. Hatta albashin da ake ɗan yaga musu daga ƙananan hukumominsu bai taka kara ya karya ba. Yanzu ma ko irin sabbin motocin nan na alfarma da wasu gwamnoni ke bai wa manyan sarakunan jihohin su, an daina jin labarin su.

Ya kamata gwamnati da ’yan majalisu su samar da wasu dokoki da za su fitar da matsayin sarakuna da martabar su a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa, don su samu bakin magana a hukumance, kuma su samu ƙarfin iko na zartar da wasu ayyuka da suka shafi cigaban jama’ar su.

Mu kuma a namu ɓangaren talakawa, ya kamata mu zama masu girmama sarakunan mu, da manyan ƙasa, tare da ba su kulawar da ta kamata, a matsayin su na manyan ƙasa, ma’abota adana tarihi da sanin darajar ƙasa. Mu sani a halin da ƙasa ke ciki, sarakunan mu ba su da wani ƙarfin ikon juya wani abu, ko sanya wa a yi dole, sai dai suna da bakin magana da isar da saƙon talakawa zuwa ga zaɓaɓɓun shugabanninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *