Martanin Labarina: Naziru Sarkin Waƙa da Aminu Saira ba su da laifi ko kaɗan

Daga Al-AMIN CIROMA

Na karanta wani labari mai taken ‘Naziru Sarkin Waƙa Ya Hayaƙa ‘Yan Jarida’ wanda da dama mutane suka mayar da martani a kafafen sadarwa, inda suka bayyana abin da fitaccen mawaƙin ya yi a matsayin tozarci da ‘yan jarida.

Babu shakka masu wannan ra’ayi suna da nasu hujjojin, bai kamata a ga laifinsu ba, sai dai ni na bambanta da mafi yawan ra’ayoyin nasu. Amma na fi karkata kan ra’ayin Malam Nazifi Dawud, wanda ya nuna yadda ‘yan jaridar da kansu suke wulaƙanta kansu.

A iya sanina dai, aikin jarida aiki ne mai ɗimbin ƙa’idoji da ‘Farillai,’ ‘Mustahabbai,’ ‘Makaruhai’ da kuma dabaru masu yawan gaske. Muddin har mutum ya kuskure su, ko ya jahilce su, shakka babu zai faɗa cikin matsala, har ma ya jawo wa kansa da ma sauran masu sana’ar jangwangwama. Kan haka ne nake ganin akasarin masu kiran kansu ‘yan jarida a yau suke cikin garari.

To, bari mu koma kan zancen da Sarkin Waƙa ya yi a cikin fim. Abu na farko da zamu kalla shi ne, labari ne ya bi, a matsayinsa na jarumi a cikin shirin. Wanda kuma a farkon farawa ma, wasu gogaggun marubuta ne suka raba dare, suka jajirce suka tsara shi. A cikin su ma, har da ma wasu manyan ‘yan jaridar. Saboda haka, ni ban ga dalilin da za a ɗora laifi kan jarumin ba.

Abin da ya kamata a yi shi ne a fahimci cewar Naziru Sarkin Waƙa fa ‘script’ ɗin labarin ne ya bi, kamar yadda aka tsara, aka ba shi.

A ganina, da yawa daga cikin masu wancan ra’ayin sukan fassara rayuwar mawaƙin ne na zahiri, wanda a ganinsu wataƙil zai iya wulaƙanta mutane, saboda sun san attajirin mawaƙi ne, wanda kuma hakan babban kuskure ne!

Na biyu kuma masu danganta laifin da Darakta Aminu Saira, su ma alwalar tasu ta sami ‘Lam’a’. Domin kuwa kafin a shiga lokeshin, sai dai marubuta labarin da ma’aikata shirin gaba ɗaya, da ma wasu ƙwararru, suka zauna suka yi bitarsa daidai gwargwado.

To, idan muka tattaro waɗannan hujjojin, babu yadda za a yi mu danganta laifin ga waɗannan bayin Allah.

Ta yaya za mu kalli aikin ɗin jarumi a cikin fim, mu yanke ma sa hukuncin zahirin rayuwarsa? Kenan duk labaran da wasu jaruman suka yi a kan wasu gungun mutane, su ma sai an yi musu hukuncin furucinsu kenan?

Sau nawa ake nuna gurɓatattun ‘yan sanda a fim? Sau nawa ake nuna alƙalai marasa adalci a wasu kotunan a fim? Shin mun taɓa jin wani ɗan sanda ya fito ya ce an ci zarafin ɗan sanda a cikin fim? Tilas ne a nuna ‘Character’ a cikin fim, mai kyau ko akasin hakan domin wataƙila a cikin fim ɗin har a bayyana wa masu kallo dalilin bijiro da ‘Character’ ɗin. Ba mamaki a cikin fim ɗin, za kuma a samar da wani ɗan jaridar da ba ya tsayawa ya karɓi na mota a wulaƙance.

Yanzu bari mu koma zahirin rayuwar wasu ‘yan jarida a wannan zamani. Dukkanin mai hulɗa da ‘yan jaridar a yau, zai yarda da ni cewar Naziru Sarkin Waƙa, ko kuma in ce Fitaccen Darakta Aminu Saira sun yi daidai, saboda ko shakka babu akasarin masu aikin jarida, sun koma tamkar maroƙa da sunan aikin na jarida.

Mafi yawa ba su da ƙwarewar aiki, sun ɗauka aikin jarida wata dama ce ta tara dukiya ko neman arziki ko ta halin ƙaƙa!

A matsayina na ƙaramin ɗan jarida, ina ƙyamar masu aikata hakan, kuma wannan lamari da ya faru, ya hasko min wata hanya zan jajirce wajen gina labari kan gurɓatattun ‘yan jaridar, waɗanda a duk sanda suka yi aiki, ba za su kama gabansu ba, sai su koma gefe suna jiran na mota! Bissalam.