Martinez ya zura ƙwallaye daidai da na Maradona a Argentina

Lautaro Martinez ya yi kan-kan-kan da Diego Maradona a yawan zura ƙwallaye a Argentina, bayan da ya zura ɗaya a ragar Peru a Buenos Aires.

Argentina ta karɓi baƙuncin Peru a wasan neman shiga gasar kofin duniya da za a buga a 2026 a Amurka da Canada da kuma Meɗico.

Martinez, mai shekara 27, ya ci ƙwallon daga bugun da Lionel Messi ya yi masa, bayan minti 55, na 32 da ya zura a raga kenan a karawa 70.

Ƙyaftin ɗin Inter Milan yana mataki na biyar tare da Maradona a jerin waɗanda ke kan gaba a ci mata ƙwallaye, Messi ne kan gaba da 112 a raga.

Talla

Gabriel Batistuta ne na biyu a yawan ci wa Argentina ƙwallaye, sai Sergio Aguero da kuma Hernan Crespo a jerin ’yan huɗun farko.

Shi kuwa Messi mai taka leda a Inter Miami, mai shekara 37, ya yi kan-kan-kan da ɗan wasan Amurka, Landon Donovan a matakin kan gaba a yawan bayar da ƙwallo a zura a raga, kowanne yana da 58.

Da wannan sakamakon Argentina tana ta ɗaya da tazarar maki shida a shiyyar Kudancin Amurka a wasannin neman shiga gasar kofin duniya, saura wasa shida suka rage.

Ita kuwa Brazil tashi ta yi 1-1 da Uruguay a Salɓador a wasan na neman shiga babbar gasar tamaula ta duniya.

Kenan Brazil tana ta biyar a kan teburi, inda ’yan shidan farko kan wakilci Kudancin Amurka a gasar ta kofin duniya.