Marubuci ne ke riƙe da fim bakiɗaya – Mubarak Dakta

“Sai an janyo marubuta jiki, an maIda su mutane ne za a ci moriyar harkar fim”

Daga AISHA ASAS 

A wannan sati, shafin Nishaɗi na Blueprint Manhaja ya karɓi baƙuncin wani haziƙin matashi, wanda ya samu shuhura a ɓangaren rubutun fim. Matashin, wanda ya ƙware ba a iya rubutun fim ba kaɗai, har ma da na zube, ya bayyana wa Bleprint Manhaja yadda ya fara da kuma finafinan da ya rubuta, kafin ya yi bayani kan muhimmancin marubuci a harkar fim da kuma irin yadda ake tauye marubuci a masana’antar finafinai. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Mubarak Idris Abubakar, wanda ka fi sani da Mubarak Dakta.

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin baƙon namu.

DR. MUBARAK: Sunana Mubarak Idris Abubakar wanda aka fi sani da Dr Mubarak. An haife ni a garin Kano, a Ƙaramar Hukumar Dala. Na yi karatun firamare da sakandire duk a nan Jihar Kano, sai a matakin gaba da sakandire inda na tafi makarantar koyon aikin lafiya da ke Jihar katsina.

Ka kasance marubuci. Ko za ka sanar da mu ɓangaren da ka fi raja’a a harkar ta rubutu?

Eh to, zan iya cewa kowanne ɓangaren na kan yi rubutu akai musamman idan halin hakan ya taso, sai dai in ba a samu jigo ba. Kawai abinda na sani indai akwai saƙo to zan yi ƙoƙarin cusawa ta yanda zai isa.

Ba mu labarin yadda ka fara yin rubutunka na farko?

Na tsinci kaina da fara rubutu a lokacin da ban zata ba, don kawai ni dai Ina karatu ne ban kuma taɓa sawa a raina zan zama marubuci ba, sai dai yau da gobe ta sa rana tsaka na tsinci kaina da ƙirƙirar jigon da na fara rubutun littafi akan shi ‘Ni Na Ga Rayuwa’.

Wane fim ka fara rubutawa, kuma ya aka yi har ka rubuta shi?

Fim ɗin da na fara rubutawa ba zan iya tuna wanne ba ne gaskiya, na san dai na yi ƙoƙarin koyar yanda ake rubutun da neman shawara daga magabata, sai dai zan iya cewa cikakken wanda ya zama na farko har aka yi sa shi ne ‘Rai Kan Ga Rai’.

Shin mene ne ya bambanta rubutun zube da kuma na fim?

Ƙa’idoji su ne kan gaba. Domin kai tsaye zubi da tsarin rubutun fim da zube ba haɗi ko kaɗan ƙa’ida ɗaya in ka sava cikin ƙa’idojin rubutun fim ka sauka daga layi.

Wacce shekara ka fara rubuta fim?

Shekarar dubu biyu da sha shida 2016.

Zuwa yanzu ka rubuta finafinai nawa?

Gaskiya ba laifi an ɗan yi rubutun tunda wasu ba ma mutum ɗaya ba ne na haɗaka ne da za a haɗa marubuta a yi. Amma ba za su haura goma ba dai wanda na rubuta ni kaɗai su ne kamar; ‘Laure’ fim ne mai dogon zango, ‘Mage da Wuri’, ‘Musaya’, ‘Baban Ladi’, akwai su ‘Rai Kan Ga Rai’, da ‘Ba Farkon Ba’, ‘Gudun Asali’, da dai sauransu

Tsakanin rubutun zube da na fim wane ne ya fi ba ka wahala?

Rubutun zube ya fi bani wahala a yanzu gaskiya saboda kafin na yi guda ɗaya na yi na fim goma. To gabaɗaya sai ya zame min kamar sabo.

Shin kana rubuta labarai ne ka yi wa masu shirya fim tayi, ko kuwa kana jira ne har sai su sun nemi ka rubuta masu?

Gaskiya sai an saka ni nake yi, shima sai mun yi ciniki, na ga an biya ni yanda nake ganin zan iya yi.

A harkar fim, marubuci ne babban jigon tafiyar, sai dai wasu marubutan da dama suna kukan ba a cika ba su wannan darajar da suka cancanta ba. A ɓangaren ka ya lamarin yake?

Har yanzu ba a ba su wallahi, dan in ba jan ido ka yi ba ma haƙƙin ka ma sai yaƙi fita. Na rasa dalilin da ya sa aka maida marubuta koma baya a harkar fim ba,  babu wata babbar daraja da suke iya tutiya da ita ta zahiri.

Akwai kuma matsala ta rashin biyan marubutan finafinai haƙƙinsu cikin jin daɗi da wasu ke faɗa. Shin ya gaskiyar maganar?

Gaskiya haka ne, mutum ne zai sa marubuci ya masa rubutu, amma ya gaza biyan shi haƙƙinsa. ‘Producer’ ne zai gaza biyan marubuci kuɗin da bai haura 100k ba, amma ki ga ya kwashi sama da ‘millions’ ya fita aiki. Ni yanda nake gaskiya kafin na fara yiwa mutum rubutu sai ya bani kaso hamsin bisa ɗari na kuɗin, ina gama rubuta rabi, da na ɗan ƙara da kaɗan nake dakatawa na nemi ciko. Dan an ce kunyar mara kunya asara ce.

Shin kowanne marubucin zube na iya rubutu fim?

Eh sosai kuwa, da yawan marubutan fim na yanzu marubutan zube ne suka koma fim. Musamman faɗuwar kasuwar littafi a duniya.

Idan har ana so a ƙara inganta harkar fim a Ƙasar Hausa, wacce irin gudunmawa ka ke ganin marubuci zai iya bayarwa a tafiyar?

Marubuci shi ke da gudunmawa ai tunda ko a yanzu marubutan ke riƙe da fim ɗin gabaɗaya, in da ba su labaran ma ba za su inganta ba. Don haka dole marubuta na buƙatar a ja su a jiki a maida su mutane domin cin gajiyar harkar.

Ta yaya za a iya taimaka wa marubuci don ganin ya samar da labari mai ma’ana?

Kowanne labari mai ma’ana yana da alaqa ta jigon da aka ɗauko. Akwai jigon da kana ji za ka san ba shi da wata ma’ana ta kusa ko ta nesa. Saboda haka in ka ji wani jigon ko da a burkice yake indai yana da ma’ana salo da sarrafa harshe na iya ɗora shi a layi har ya inganta.

Daga fara rubutunka zuwa yanzu, waɗanne irin nasarori ka samu?

Alhamdulillahi nasarori an same su, musamman ta ɓangarorin gasa da aka dinga yin nasara. Sai kuma rufin asiri na yau da kullum wanda kaso 75 rubutu ne gaskiya.

Waɗanne ƙalubale ka dinga cin karo da su kawowa yanzu?

To ƙalubale suna da yawa duk da dama komai na rayuwa ya gaji hakan. Muna kuma kallon haka a matsayin wasu matakan nasara domin sai an ƙalubalance ka a wasu ɓangaren ka ke iya gyarawa.

A harkar rubutu ko kana da ubangida da ya fara ɗora ka kan hanya?

Gaskiya babu, ba zan iya nuna guda ɗaya yanzu na ce, shi ne ubangida na ba. Akwai dai iyaye da yayye a rubutun da muke kallo a madubi ake kuma neman shawara ko gyara in buƙatar hakan ta taso.

Wane irin buri ka ke da shi a harkar rubutun fim?

Yanda muka fara lafiya Allah ya sa mu gama lafiya. Allah ya kiyaye mu daga tsara abinda ba zai kawo gyara ga al’umma ba. Fatan duk abinda za mu rubuta ya zama alkhairi ga kowa.

Bari mu koma ɓangaren marubuta a Intanet. Wasu na cewa, zuwan nasu ya gurgunta kasuwar rubutu, ciki kuwa har da rubutun finafinai. Shin menene gaskiyar wannan zancen?

Eh, ba zuwan su ba ne ya gurgunta kasuwar ba. Zuwan intanet shi ne ya karya kasuwar littafi, shi kuma Allah shi ke da zamani, don haka duk abinda zamani ya zo da shi bai kamata a ƙi karɓa ba, sai dai a bi bisa ƙa’ida kar son zuciya ya shiga. Amma batun gurguntawa da ace marubutan sun yi wani tsarin da ko ba a tafi gabaɗaya ba, qila a samu wani kason kasuwar ya maƙale ta hanyar zahiri kaso hamsin intanet ɗin kaso hamsin.

Da yawa masu rubutu sun bi zamani ta hanyar saka labaransu a kafafen sadarwa. Shin kana ɗaya daga cikin waɗannan marubuta?

Gaskiya bana ciki, don ba zan iya cewa ga ƙwaƙƙwaran labari guda ɗaya nawa da na saka ba. Saboda wasu dalilai.

A naka ɓangaren, zuwan marubuta onlayin cigaba ne ko ci baya?

Marubutan onlayin su yarda ɗaliban marubuta published ne. Su bisu su kwantar da kai su ji me aka yi jiya me ya kamata ayi yau da gobe. In aka ba wa babba girma za a iya haɗa kai domin ganin an kawo qarshen matsala kowacce iri ce.

Ta wacce hanya ka ke ganin za a iya kawo ƙarshen rubutun batsa da ya yawaita tsakanin marubuta onlayin?

Zamani ne ya zo da su kuma shi zai gaba da su ɗin. Duk abinda kuma ya cimma lokaci ba a jayayya da shi. Kawai dai rashin iya kafa kai da ginin gobe na marubutan online shi za a kira ci baya domin ba su ɗau hanyar da za su kai ga nasarorin da marubutan kasuwa suka kai ba.

Mun gode.

Ni ma Na gode.