Marubuta a yanar gizo ba su ƙwace damar marubutan littafi ba – Hafiz Koza

“Makaranta za su iya taka rawar tsaftace rubutu”

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda mu ka sani, rubutu da marubuta sun karkasu da dama, wasu ta su baiwar kan tsara labarai ne irin na zube, yayin da waɗansu suka zama gwanaye ta ɓangaren wasan kwaikwayo, wasu kuwa rubutacciyar waƙa ce aka hore masu iya tsarawa da aika saƙon zuciyarsu cikin siga mai jan hankalin mai karantawa. Sai dai a wasu lokuta akan samu ‘yan baiwa ko a cikin duniyar baiwa, domin wasu daga cikin marubutan na samun damar zagaye a tsakanin nau’ukan rubutu ba tare da an kira su da baƙi ba. A wannan satin shafin Adabi ya yi nasarar zaƙulo mu ku ɗaya daga cikin waɗannan marubuta da ke iya haɗa taura biyu su tauna a lokaci ɗaya. Hafiz Adamu wanda aka fi sani da Hafiz Koza, marubuci ne da ke da muhalli a rubutu na zube da kuma rubutacciyar waƙa. A tattaunawar mu, mai karatu zai ji ma’ana da kuma ƙa’idojin rubutacciyar waƙa tare kuma da banbancin ta da rubutu irin na zube. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da marubuci Hafiz Koza:

BLUEPRINT MANHAJA: Mu fara da jin tarihinka a taƙaice.

HAFIZ KOZA: Sunana Hafiz Adamu, an haife ni a garin Koza da ke ƙaramar Hukumar Mai’aduwa, Jihar Katsina. Na yi karatu a Koza da Daura da kuma Katsina.

A wane ɓangare na marubuta za ka iya kiran kanka?

Idan na fahimci tambayar ana nufin tsakanin zube da waƙa da wasan kwaikwayo a wane ɓangare rubutuna ya fi ƙarfi? Idan haka ne, to zan iya cewa na fi ba da kai a fagen rubutacciyar waqar Hausa, duk da haka nakan yi zube a wasu lokutan. A taƙaice gidaje biyu a cikin uku na fi mai da hankali gare su, wasan kwaikwayo sai dai ko a nan gaba idan hali ya ba da.

Wacce shekara ka fara rubutu?

Na daɗe Ina jarraba yin rubutu, amma a wajajen shekarar 2013 zuwa 2014, lokacin Ina karatun difiloma ne na tsinci kaina a wani rukuni na marubuta Hausa, a guruf ɗin Duniyar Marubuta da ke ‘Facebook’. Daga wannan lokaci na rinƙa amfani da wannan kafa wajen isar da saƙonnin rubuce-rubucena ga al’umma.

Ba mu labarin rubutunka na farko, wato waƙa ko labarin da ka fara rubutawa tare da dalilin rubutun.

Waƙar da na ke iya tunawa wadda na fara rubutawa, ƙasida ce ta yabon Sheikh Abdurraƙi Kousa, wani mashahurin malami ne da ya rayu a garin Kousa da ke Jihar Damagaram a Jamhuriyyar Nijar. Rubutun zube kuma na fara da wani labari ne da na ba sunan ‘Dr. Nafisatu’, yana ba da labarin wani yaro ne maras galihu da aka so vata wa rayuwa tun yana ƙarami, daga baya abubuwa suka afku har aka ci galaba kansa, ya rasa ransa, a daidai wannan lokaci ne ita kuma Dr. Nafisatu ta shigo cikin lamarin wanda ya yi sanadin bankaɗo abubuwa masu tarin yawa a rayuwar shi wancan yaro da kuma ita kanta. To amma fa har kawo yanzu labarin ba a wallafa shi ba a kowacce siga, wato littafi bugagge ko a ‘intanet’.

Me ya kamata marubuci ya samu a lokacin da ya shiga wata ƙungiya ta marubuta?

Idan aka haɗu an fi cimma nasara a duk abin da aka sanya gaba. Ƙungiya tana ƙunsar manya da ƙananan marubuta, don haka ta zama wajen renon sababbin marubuta. A ƙungiyance za a iya tunkarar cikas da ƙalubale idan ya tunkaro harkar rubutu, saɓanin idan ya zo ana zaman ‘yan marina sai ya ƙara kassara hidimar ta rubutu. Kaɗan daga cikin alfanun da zan iya kawowa kenan a taƙaice.

Wasu daga cikin marubuta littafan Hausa na ɗora alhakin rugujewar kasuwarsu kan marubuta a yanar gizo. Menene naka ra’ayi?

Idan kiɗa ya sauya to rawa ma ya kamata a ce yadda ake taka ta ya sauya salo. Ina son in ce ba wani da za a ɗora wa alhakin rugujewar kasuwar littafi, tun da ba a yi ma kowanne marubuci iyaka da yaɗa fasaharsa ba.

Me zai hana marubutan da ke ƙorafin an kashe masu kasuwa su mai da hankali wajen sajewa da zamanin domin morar abin da ya zo da shi? Hanya ce mafi sauƙi ta aika saƙo aka zo da ita, kenan bai kamata a dunƙule hannu a zuba idanu ba tare da an yi amfani da ita ba. Marubuta bakiɗaya za su iya juya akalar rubutunsu zuwa ‘intanet’, hakan shi ne zai rage ƙorafin ana cin kasuwa ba da wane ko wance ba.

Na san wasu mashahuran marubuta litattafan Hausa da suka yi caffa ga rubutu a ‘intanet’ kuma suna amfana da hakan. To amma fa ni ban ce a daina rubuta labari a takardu ba, Ina cewa a rinƙa haɗa guda biyun ana tafiya da su a lokaci guda ne. Yin haka zai sa rubutu ya zama ragon malam, ga kitse ga arha.

Shin me ake ce wa rubutacciyar waƙa?

Masana sun gama wannan aiki na bayani a kan me ake ce wa rubutacciyar waƙa. Daga abin da suka bayyana sai na fahimci rubutacciyar waƙa a matsayin wata hanya ta aika wa da saƙo, wadda aka gina a bisa tsararriyar ƙa’ida tare da zaɓen kalmomi da daidaita su da amfani da su ta yadda suka sha bamban da magana wacce ta ke kara-zube, kuma a rubuce.

Menene banbancin ta da rubutun zube?

Na farko dai suna ya bambanta su, wato wannan waƙa ce wancan kuma zube. Bayan haka idan aka ce zube a rukunin adabi ana nufin labaran Hausa ne da aka rubuta su ba tare da kiyaye wasu ƙa’idoji da akan samu a waƙa ba. Ita waƙar nan an ce tana da tsararriyar ƙa’ida, to amma shi zube ai ba a shimfiɗa masa wasu ƙa’idoji da za a gina shi a kansu ba. Ina ganin su waɗannan ƙa’idoji da akan samu a waƙa sun ba mu hasken cewa, lallai waƙa da zube abubuwa ne mabambanta.

Shin ko akwai wasu dokoki da ya kamata marubucin waƙe ya san su kafin ya fara rubutun?

To yauwa! Na ji daɗi ƙwarai da aka yi wannan tambaya, domin amsa ta zai ƙara fito mana da banbanci tsakanin zube da waƙa. Ita rubutacciyar waƙa tana da wasu abubuwa da matarka ko manazarta ke tsefewa idan an zo batun yi mata tarke ko nazari. Muhimman abubuwan su ne, fasalin baitoci, wato waƙa gwauruwa ce ko ‘yar tagwai, har abin da ya kai ga batun tarbi’i da tahamisi.

Sauran dokokin kuwa sun haɗa da ƙafiya ko amsa-amo kamar yadda wasu ke cewa. Akwai kari, wato bahari, wanda za a same shi can ga masana aruli. To waɗannan suna daga cikin dokokin rubutacciyar waƙa da za a iya kawowa a fira mai wa’adi irin wannan.

Kodayake Ina cin karo da wasu rubutattun waƙoƙin Hausa da suke saɓa wa duk waɗannan ƙa’idoji, idan na tambaya me ya faru? Sai a ce da ni ai sabon salon waƙar Hausa ce da ake kira Ballagaza. Ai kuwa duk inda aka ji Ballagaza za a fahimci abun bai kai ya kawo ba.

Wasu sababbin marubuta na ɗora laifin rashin ingancin rubutunsu kan tsofaffin marubuta. A cewar su, su ne ba su ba su taimakon da suke buƙata. A matsayinka na wanda ya kwana biyu a harkar rubutu, menene sahihancin wannan zance?

Ni ma ba zan hura hanci in bugi ƙirji in ce Ina cikin manyan marubuta ba, har yanzu rukunin yarinta na ke a sabgar, don haka a wannan matsayi na ƙaramin marubuci zan yi magana. Ni dai an taimake ni kuma ana kan taimako na a hidimar rubutu. AlhamdulilLahi. To sai dai ba zan ce duk ƙananan marubuta ba su fuskantar ƙalubale daga manya ba, amma lallai ga duk mai halartar tarukan da akan aiwatar na marubuta Hausa za a ga yana wahala baƙo ya rarrabe wancan babban marubuci ne wancan kuma ƙarami, saboda ana zamantakewa ta masu ilmi da mutunta juna, ba cuta ba cutarwa.

Kodayake an yi batun rashin inganci a rubutu, gaskiya wannan kwata-kwata ma ba shi da wata alaƙa da cewa tsofaffin marubuta ne ke hana rubutun masu tasowa zama ingantacce, domin shi rubutun nan fikra ce da kaifin basira, ba mamaki ɗan-bana-bakwai ya rubuta labari a ce madalla, da kyau, ƙwarewa! Yayin da wani mai shekaru a harkar idan ya rubuta kawai sai dai a ce ya yi!

Sanannen abu ne, al-kunya na ɗaya daga cikin manyan ɗabi’u na malam bahaushe. Sai ga shi an wayi gari marubuta a cikin yaren Hausa na ƙoƙarin kawar da wannan ɗabi’a ta hanyar yawaita rubutun batsa. A fahimtar ka, me ya janyo yawaitar rubutun batsa?

Yawaitar kallon batsa shi yake kawo samuwar rubutun batsa.

Ta wacce hanya za a iya tsaftace rubutu a yanar gizo?

Makaranta fa za su iya taka rawar tsaftace rubutu, ba ma sai na ‘intanet’ ba. Idan marubuci ya yi kamar labari uku zuwa huɗu ba amshi ko guda ba, to ai ya san bai rubuta abun kirki ba. Ashe kuwa dole ya nemi sanin yadda zai tsaftace rubutunsa a wurin masana. Amma idan ana nufin ta hanyar tacewa kafin a sake shi ga mutane, a ɗan ƙaramin sani na ba zan iya gano wannan hanya ta tsaftace rubutu a ‘intanet’ ba, saboda marubutan ne ga su nan birjik kuma kowa da wayarsa yake rubutu a ɗaki ko falo, ana kallon TV ko an tafi wurin buki; rubutu dai ake yi ba ƙaƙƙautawa a duk yadda aka tsinci kai, ashe kuwa bin waɗannan mutane a ce ku zo a tace ko a tsaftace ma ku rubutu kafin ku sake shi, kai! Ni ban san ta ina za a fara wannan ba.

Za mu iya sanin wasu daga cikin waƙoƙin da ka rubuta?

Me zai hana! Da yake rubutattun waƙoƙi ba kamar waɗanda akan rera ba ne, wataƙil sai dai kawai a ambace su, domin ba lallai ne a samu mutane da yawa masu karanta wannan fira da suka san waƙoƙin. Zan dai bayyana wasu daga ciki, kamar waƙar da na rubuta babu daɗewa a kan yayye maza a cikin gida su kula da ƙananan buƙatu na ƙannensu mata, musamman a kan ba su kuɗi domin sayen audugar mata da aka ɗauka ba a bakin komai ba.

Wannan ma shi ne jigon waƙar, na sanya mata suna ‘Sanitary Pad’, amma fa da Hausa na rubuta ta a shekarar 2022 ɗin wannan. A can shekarun baya, wajajen 2013 zuwa 2014 na rubuta wata waƙa mai fayyace wuraren raba kalma da haɗe su a rubutun Hausa. Sunan waƙar ‘Gyara Rubutunka A Waƙe.’ Akwai waƙar ‘Ƙasata’ wadda na rubuta don kishin ƙasa.

Ina tune da ‘Tarbi’in Waƙar Arewa Jamhuriyya Ko Mulukiyya?’. Ga wata ma wadda na rubuta domin ta’aziyyar rashin Mai Martaba San Kano, Alhaji Ado Bayero (Allah ya jaddada mashi rahama) tare da taya Sarki Muhammadu Sanusi ll murnar hawa karaga duk a lokaci guda. Zan tsaya haka.

Labarai fa?

Me zai hana! To da yake labarai da nakan rubuta irin gajeru ne masu ɗauke da wasu darussa, zan iya tunawa da labarina mai taken “Rikicin Makiyaya da Manoma, Ina Mafita?” Akwai wani kuma da na ba suna “Hausa…” Ga wani ma da na kira shi da “Hinde Matar Ilu.”

Tsakanin rubutun waƙe da zube wane ka fi sha’awar yi ko in ce ya fi sauƙi a wurin ka?

Na fi sha’awar rubuta waƙa kuma ta fi yi mani sauƙi. Ba na ce ga dalili ba, amma lallai haka abun yake.

Ko akwai kiran da za ka yi ga manyan marubuta?

Manyan marubuta su ci gaba da kyautata zamantakewarsu ga ƙananan da ke tasowa, saboda su ne masu gadon kujerarsu idan girma ya zo ko ta Allah ta kasance gare su. A girmama kai a yi ƙoƙarin tsaftace mu’amala ta fili da voye wadda ka iya shigowa a tsakanin manyan da ƙanana da ma sauran al’umma bakiɗaya. Duniya tana kallon marubuci a matsayin wani muhimmin taliki mai kawo gyara, to don haka ɗabi’unsa wajibi ne su wakilce shi a zukatan jama’ar da ke kallonsa a matsayin karimi.

Wacce shawara za ka ba wa marubuta masu tasowa?

Ina da shawarwari ga marubutan da ke tasowa. Ya kamata mu yi ƙoƙari wajen inganta rubutu ta hanyar yin sa a cikin salon armashi. Mu ba da himma ga yin rubuce-rubucen kishin ƙasa da nemo hanyoyin kyautata shugabanci da ƙarfafa zuciyar al’umma su zama jajirtattu wajen nema da biɗar na kansu. Kar marubucin da ke tasowa ya zama mai kwaɗayi da son ba kansa girma da nuna cewa shi ma karansa ya kai tsaiko, a dai tafi a hankali har a cimma nasara.

Marubuci mai tashe ya sa himma ƙwarai ya kuma yarda da kansa lallai zai iya rubuta abin da zai sauya tunanin al’umma daga rauni zuwa ƙarfi, daga munin aiki zuwa kyakkyawa, daga ruɗani zuwa sa’ida, daga firgici zuwa salama da makamantan haka.

Ka da marubuci mai tasowa ya kuskura ya sa a ransa cewa, zai yi kuɗi ko suna ta hanyar rubutu, ana samun duk waɗannan a rubutu ba makawa, to amma Ina ganin a sa ran yin rubutu wata hidima ce ta al’umma ba domin a more ta kawai ba.

Mun gode.

Ni ma na gode ƙwarai.