Marubuta su kasance masu zurfafa bincike – Shugaban Ƙungiyar Mikiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙungiyar Marubutan Jihar Kaduna, wadda aka fi sani da ‘Mikiya Hausa Writers’, Kwamared Sani Shehu Lere ya yi kira ga ɗaukacin marubuta da su kasance masu zurfafa bincike kafin aiwatar da rubutun su.

Sani ya yi wannan kiran ne a wani taron ƙara wa juna sani da ƙungiyar ta shirya kuma ta gabatar a makon jiya. A cikin jawabin sa Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu ya ce yin bincike bayan samuwar jigon yin kowane irin rubutu na hikaya abu ne mai muhimmancin gaske, musamman wajen kauce wa kura-kurai na zahiri da kowa zai iya ganinsu a bayyane.

Lere ya ƙara da cewa, “Yanzu duniya ta zama sabon yayi, ba kamar da ba, wanda sai dai mutum ya zauna ya yi rubutu da tunanin sa kaɗai, saɓanin yanzu da ilimi ya wadata ta kowane ɓangare.”

Ya ce, “Yana da kyau idan marubuci zai yi rubutu a fannin kiwon lafiya ko ɓangaren shari’a ko kuma wani ɓangare da ya shafi kimiyya da fasaha, to ya kasance marubuci ya tuntuɓi masani a wannan ɓangaren don ya yi masa ƙarin haske akai.”

A ƙarshe ya kuma shawarci marubuta su dinga rubutun ilimantarwa da faɗakar da al’umma illolin ta’addanci da shaye-shayen kayan maye da sauran ɓangarori don gyara tarbiyyar al’ummar ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *