Marubutan baya sun fi na yanzu juriya da amsar gyara – Gidan Dabino

*Fitowar rubutu a yanar gizo ya sa kowa na iya kiran kan sa marubuci – Gidan Dabino

Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Arewacin Nijeriya, sannan mai shiryawa da bayar da umarni, sannan ɗan wasa ne a shirin fina-finan Hausa kuma ɗan jarida. Kusan zan ce idan an kirashi da ɗaya daga cikin ubanin Adabin Hausa ba a yi kuskure ba, domin ya kasance a jerin farko da su ka reni adabin zamani, su ka yi ma sa sutura tare da kula da ingancin sa. Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ne Shugaba kuma Daraktan Gudanarwa na kamfanin Gidan Dabino International Nigeria Limited.
A wannan satin manhaja ta yi nasarar kawo maku shi a wannan fili namu na adabi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Daga AISHA ASAS

Masu karatu za su so jin tarihin ka.
An haife ni a shekara ta 1964 a garin Ɗanbagina da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Na girma a Unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano. Na fara karatun allo, (Alƙur’ani) a makarantar marigayi Malam Rabiu a Unguwar Zangon Barebari, a shekarar 1968 da karatun littattafai na Islamiyya a makarantar marigayi Sheikh Tijjani na ‘Yanmota, (1971).
Ban samu damar yin karatun boko ina ƙarami ba, sai da na girma sannan na shiga makarantar ilmin manya ta Masallaci ‘Adult Evening Classes’, Kano a shekara ta 1984 zuwa 1986. Na yi makarantar sakandare ta dare (G.S.S. Warure Evening Session), Kano a shekara ta 1987 zuwa 1990. Na shiga Jami’ar Bayero inda na samu takardar shaidar Diflomar ƙwarewa a kan yaxa labarai, wato (Professional Diploma in Mass Communication) a Sashen Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005. Ni mutum ne mai sha’awar tafiye-tafiye da rubuce-rubuce da bincike-bincike. ina da mata ɗaya da ’ya’ya biyar.

Zuwa yanzu ka rubuta littafai nawa?
Na rubuta littattafai da aka buga su kamar haka: ‘In Da So Da Ƙauna’ 1-2, ‘Masoyan Zamani ‘1-2, Hattara Dai Masoya’ 1-2, Wani Hani Ga Allah’ 1-2, Duniya Sai Sannu, Kaico! Malam Zalimu’ (wasan kwaikwayo), Malam Zailani’ (ci gaban Malam Zalimu (wasan kwaikwayo), Ina Mafita’ (wasan kwaikwayo), Daƙiƙa Talatin’ (wasan kwaikwayo), Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye, ‘Ina Mafita?’, Sarkin Ban Kano, Alhaji Dr. Muktar Adnan’ (tarihi), wanda na rubuta tare da Sani Yusuf Ayagi da ‘From Oral Literature to Video: The Case of Hausa’. (Takardun da mu ka gabatar a jami’a Hamburg, Jamus, ni da Farfesa Abdalla Uba Adamu).
An kuma fassara wasu daga cikin littattafaina guda uku daga harshen Hausa zuwa Turanci: ‘The Soul of My Heart’ (Fassarar In Da So Da qauna) da ‘Nemesis’ (Fassarar Masoyan Zamani) da kuma Kaico! (Fassarar Kaico!) ‘Young Women Substance Abuse and The Way Out’ (Fassarar Mata Da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita?)
Na gabatar da muƙalu da dama a tarurrukan ƙara wa juna sani a cikin Nijeriya da ƙasashen waje. Wasu daga cikin takardun an buga su a cikin kundaye (littattafai). Ina yin rubuce-rubuce a cikin jaridu da mujjalun Hausa.

Ta ɓangarem ƙungiyoyi, ko akwai wata ƙungiya da ka kafa?
Tare da ni aka kafa wasu ƙungiyoyi, kamar ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya Reshen Jihar Kano, (ANA) a shekara ta 1992, kuma na riƙe shugabancinta na tsawon shekara uku da ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano, (Kano State Filmmakers Association) wanda a halin yanzu ni ne shugaban riƙo na ƙungiyar Marubuta ta Raina Kama (Raina Kama Writers Association).

Ko akwai waɗansu shirye-shirye da ka ke gabatar wa a gidajen rediyo don wayar da kan marubuta?
Na taɓa gabatar da shirin ‘Alƙalami Ya Fi Takobi’, a gidan rediyo Freedom Kano da kuma shirin ‘Duniyar Masoya’ a gidan rediyo Shukura FM da ke Damagaram, Qasar Nijar.

Za mu so mu ji ƙasashen da rubutu ya kai ka.
Harkar rubuce-rubuce da kuma wallafa ta ba ni damar zuwa ƙasashe fiye da goma sha biyar na Afrika, sannan kuma a ƙasashen Turai na samu zuwa London da Fransa, Italy, Holland da kuma Germany.

Ɓangaren karramawa a fagen rubutu na san su na da yawa, sai dai za mu so muji wasu daga ciki.
Na zama zakaran gasar rubutun wasan kwaikwayo ta shekarar 2009 ta tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir Ƙaraye, a Abuja, Nijeriya. Na samu takardun yabo da dama daga jami’o’i da ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da gwamnati, saboda gudummawa iri-iri da na ke bayarwa waɗanda su ka shafi harshen Hausa da adabi da al’adu ta fannin rubuce-rubuce da shirin finafinai da aikin jarida da harkokin ƙungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi da kuma gwamnati. A ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2011 na samu takardar yabo daga Inuwar Jama’ar Kano, (Kano Forum) cikin mutane goma sha ɗaya da aka yaba da su a Jihar Kano wajen bayar da gudummawa game da ci gaban al’umma.
Sannan a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 2014, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karrama ni da lambar yabo ta ƙasa mai taken, Member of the Order of the Niger (MON) bisa hidimta wa jama’a da na yi a cikin ayyukana. A shekarar 2017 na samu zuwa matsayin tantancewa ta ƙarshe (nomination) a gasar finafinai ta ‘Zuma Film Festival’ da ke Abuja a matsayin jarumin jarumai na Afrika. A shekarar 2018 na samu nasarar lashe kambun jarumin jarumai har sau uku a cikin gasar ‘AMMA Award’ da ‘Kaduna International Film Festival’ da ‘Arewa Entertainment’, sannan na amshi kambin mai shirya finafinai da ya zarce kowane (Best Producer) a ‘KILAF Film Festival’ duk a cikin fim ɗin Juyin Sarauta. A shekarar 2019, na sake zama jarumin jarumai (Best Actor in Leading Rule) sannan na amshi kyautar alqalan gasa (Golden Jury Award) a gasar ‘Kaduna International Film Festival’.

Za mu so jin ƙungiyoyin da ka ke ciki na harkar rubutu.
Ina cikin wasu ƙungiyoyi kamar haka: Motion Picture Practitioner’s Association of Nigeria, (MOPPAN) da Association for Promoting Nigerian Languages and Culture, (APNILAC) da West African Research Association (WARA) da Indigenous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN) da sauransu.

Ko akwai littafan ka da ake sa ran fitowar su?
‘Ina Mafita?, Kaico!’ (Fassara zuwa Ingilishi), Young Women Substance Abuse and The Way Out, (Fassarar Mata da Shaye-Sayen Kayan Maye: Ina Mafita?), Malam Zalimu’ (Fassara zuwa Ingilishi).

Me ye bambanci tsakanin rubutun baya da kuma na yanzu?
Bambancin shi ne, marubutan yanzu suna gaggawa wajen fito da littafi, saɓanin na baya suna yin haƙuri su bayar a duba musu, a gyara musu kurakuran ciki.

Tsakanin rubutun littafi da harkar fim wane ne ka fara?
Na fara harkar rubutu da kuma wasan kwaikwayo na daɓe a lokaci daya, a shekarar 1984. Don haka ina yin su a lokaci ɗaya, daga baya kuma da aka fara finafinan na bidiyo, sai na juya littafina na ‘In D a So D a Kauna’ zuwa fim a shekarar 1994, ya fito a 1996.

Littafin ka na farko?
In Da So Da Kauna, shi ne littafin da na fara bugawa, ya fito a shekarar 1990

Ta ya ya za a iya dawo da martabar rubutun Hausa?
Sai an yi gangamin dawo da harkar karance-karance tsakanin mutanenmu, kamar yadda yake a da, kafin finafinai su zo su ɗauke hankalin masu karatu.

Littafai sun yi ƙaranci a kasuwa saɓanin ‘yan shekarun baya, ko me ye dalili?
Saboda marubuta ‘online’ sun jawo koma bayan sayar da littattafai a kantuna.

A matsayin ka na uba a harkar rubutu, wace shawara za ka ba wa marubuta ma su tasowa?
Su yi rubutu mai ma’ana, su kula da addininsu da al’adar su, su yi rubutu don ilmantarwa ba don neman kuɗi kawai ba.

Waɗanda su ke son fara rubutu har su mayar da shi littafi ta ina za su fara?
Za su fara ne da labari, bayan labari sai kuma su nemi masu duba musu don su duba su ba da shawarwari da su ka dace, don su fitar da littafi mai inganci. Sannan su nemi shawarwari ta yadda za su fito da littafin har ya isa hannu jama’a.

Ana cewa marubuta na baya sun fi yin rubutu mai ma’ana fiye da na yanzu, shin ko me marubutan da su ka fi na yanzu?
Abin da suka fi na yanzu haƙuri da juriya da biyayya, da ɗaukar gyara da shawarwari da ake ba su. Kuma suna da haɗin kai fiye da na yanzu, marubutan ba su da yawa, kusan kowa ya san kowa. Mafi yawansu ba don kuɗi suke rubutun ba. Sha’awar ta fi neman kuɗin yawa a zuciyarsu.

A duniyar rubutun Adabin Hausa ba inda za a faɗi sunan ka ba a san ka ba, ko ya ka samu wannan ɗaukakar?
Wannan abu ne daga Allah, sai kuma rubutu da na yi na littattafaina waɗanda su ka yi shuhura a lokacin da muke tashen rubutu. Mun kuma bauta wa harkar rubutun tun daga shekarar da littafina na farko ya fito, 1990 har zuwa yau 2021, shekara 31 kenan. Kin ga kuwa Hausawa suna cewa daɗewa a bauta ma ‘yanci ce.

Rubutu ya shiga wani kwazazzabon da wasu ke ganin ba ta yadda za a iya fito da shi, har ya dawo da ƙima da darajar sa. A matsayin ka na ƙwarare kuma wanda ya jima a duniyar rubutu, ya ka ke hangen wannan matsalar?
Ai Allah shi ne mai zamani, kuma komai da lokacinsa, fitowar wayoyi sun taimaka matuƙa wajen kawo koma bayan bugaggun littattafai. Saboda yanzu kowa ma ya na iya kiran kansa marubuci a ‘online’, da wanda ya san darajarsa da wanda bai san darajarsa ba, da marubucin da ma wanda ba marubucin ba. Saboda haka wannan matsalar ban san ta yadda za a iya shawo kanta ba, face mu jira mu ga yadda Allah zai yi wani sauyin, ko za a samu dawowar darajar tasa, ko kuma ya tafi kenan? Allah ne masanin yau da gobe da jibi da kullum.

Zuwa yanzu ka cika burin da ka ke da shi kan rubutu, ko da saura?
Alhamdu lillahi, na samu abin da na samu daga cikar burina a rubutu, domin lokacin da na fara ban zaci zan kai yadda na kai ba. Sai kuma Allah ya yi ikonsa na wuce yadda ko a mafarki ban taɓa kawowa zan kai ba.

Inda So Da Ƙauna, ƙagaggen labari ne?
Ba 100 bisa 100 yake ƙagaggen labari ba, akwai wasu wuraren abin ya faru a zahiri ne, sai dai an ɗan yi kwaskwarima saboda wasu dalilai.

A lokacin da ka fitar da littafin ka na farko, ka fuskanci matsaloli kafin buga shi?
Ƙwarai kuwa, na fuskanci matsaloli na rashin kamfanin da zai iya ɗaukar nauyin bugawa ba tare da na ba da kuɗi ba, wato a karɓa a buga ana ban kamisho, abin ya gagara sai da na nemo N5000 a shekarar 1990 sannan na buga littafin guda 1000, na sayar da shi N8000. Ta haka na fara.

Nasarorin da ka samu a harkar rubutu ba za su ƙirgu ba. Duk da haka za mu so jin waɗanda ka ke alfahari da su.
Suna da shahara da ɗaukaka a duniyar rubutun adabin Hausa a gida da wajen Nijeriya. Tafiye-tafiye zuwa ƙasashe sama da ashirin duk saboda rubutu. Samun lambar yabo ta MON daga Gwamnatin Tarayyar Nijeriya a shekarar 2014. Wanda a cikin marubuta adabin zamani, ni ne mutum na farko da aka fara bai wa ita.

Wane ka fi sha’awa a yanzu tsakanin rubutu da Fim?
Rubutu.

Wasu marubuta na ganin rashin samun tallafi daga gwamnati ne ya hana su kai wa ga irin nasarar da marubutan baya su ka cimma, ya ka ke kallon wannan zancen?
To, marubutan irin su Abubakar Imam kenan. Amma ba irinmu ba, domin ire-irenmu babu wata gwamnati da ta ba mu tallafi, mu da kanmu muka yi fafutukarmu har muka kai ga samun nasara. Don haka ba na zaton sai gwamnati ta ba ka tallafi za ka yi nasara, nasara daga Allah take, amma kuma taimakon gwamnatin ya na daɗa taimaka wa wasu su samu damar fito da rubuce-rubucen su, har su kai ga isa hannu mutane a faɗin duniya.

Mun gode.
Nima nag ode.