Masana kimiyyar ƙasar Sin sun gano wani sabon ma’adini da aka ɗauko daga duniyar wata

Daga CMG HAUSA

Masana kimiyya na ƙasar Sin, sun gano wani sabon ma’adini da aka sanyawa suna Chang’esite-(Y), wanda kumbon Chang’e-5 ya kwaso daga duniyar wata.

Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, da hukumar lura da ayyukan binciken samaniya ta ƙasar ko CNSA, da hukumar lura da makamashin Atomic ta ƙasar ko CAEA suka fitar a Juma’ar nan, an ce an tantance sabon ma’adinin ne bayan zurfafa binciken kimiyya.

Da yake karin haske kan hakan, mataimakin daraktan hukumar ta CAEA Dong Baotong, ya ce wannan ne karon farko a tarihi da ƙasar Sin ta gano wani ma’adini a duniyar wata, kuma karo na 6 da dan Adam ya cimma nasarar yin hakan.

Da wannan sakamako kuma, ƙasar Sin ta zamo ƙasa ta 3 a duniya, da ta taba yin nasarar gano sabon ma’adini a doron duniyar wata.

Ma’adinin Changesite-(Y), dutse ne mai yanayi irin na ƙanƙara.

Kuma tuni sashen tantance sabbin ma’adinai da sanya musu sunaye, dake ƙarƙashin babbar hukumar masana albarkatun ma’adinai ta duniya, ta amince da sabon ma’adinin a hukumance.

Mai fassara: Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *