Masana sun ɗora laifin ambaliya kan al’umma da kuma watsi da gargaɗin NiMeT

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu ƙwararru masu fafutukar kare muhalli sun ɗora matsalar ambaliya kan halayyar wasu ‘yan ƙasa da ke toshe magudanan ruwa da bola, gami da gini a kan hanyoyin ruwa, lamarin da ke haifar da ta’azzara ambaliya a cikin al’umma da garuruwa.

Ƙwararru a wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya gudanar a yankin Kudu maso Kudu sun kuma ɗora laifin a kan rashin kula da shawarar gwamnati a kan lamarin.

Sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da hasashen ambaliyar ruwa da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya, NiMeT, da Hukumar Kula da Ruwa ta Nijeriya ke yi.

Masanan sun kuma ci gaba da cewa rashin aiwatar da dokokin tsare-tsare na gari da rashin aiwatar da waɗanda ake da su na daga cikin abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa.

A cewarsu, wasu jihohin suna da dokokin da ba su da tushe, yayin da wasu kuma ba za su iya aiwatar da su ba saboda cin hanci da rashawa.

Ƙwararrun sun ƙara da cewa waɗannan kura-kurai sun haifar da ɓarna sosai a ƙasar domin an yi hasarar rayuka da dukiyoyi da dama tare da rasa muhallai.

Sai dai sun buƙaci gwamnati da ta gaggauta ɓullo da matakan kariya a matakin jiha da tarayya domin shawo kan matsalar.