Masana sun yaba wa hulɗar Sin da Afrika a fannin fasahohin makamashin rana

Daga CMG HAUSA

Masana da masu tsara manufofi, sun yabawa hulɗar dake akwai tsakanin Sin da Afrika a fannin amfani da fasahohin makamashin hasken rana.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, darakta janar na ƙungiyar ƙawance kasashe domin amfani da makamashin rana ta duniya (ISA), Ajay Mathur, ya jaddada muhimmancin hulɗa da Sin da ɗimbin damarmakin da hakan ke da shi wajen cimma burin nahiyar Afrika na raya makamashin hasken rana.

Da yake bayyana ƙarancin samar da ƙananan turakun makamashin hasken rana a duniya, Ajay Mathur ya yi kira ga kamfanonin ƙasa da ƙasa, su mayar da hankali wajen samar da tashoshin makamashin hasken rana da ba su dogara da turakun lantarki ba a nahiyar, domin jama’ar dake yankunan karkara da wurare masu nisa su amfana.

Ya ce ƙasar Sin ce ke kan gaba wajen samar da kayayyakin samar da makamashin hasken rana a fadin duniya, musamman a Afrika. Yana mai cewa faifan samar da lantarki daga hasken rana wato Panels da baturan da ake amfani da su a Afrika, sun fito ne daga ƙasar Sin.

A cewarsa, nahiyar na da ɗimbin damarmakin makamashin da ake iya sabuntawa, ciki har da arzikin hasken rana.

Ƙungiyar ISA ta gudanar da taron kwamitin shiyya karo na 4 ne a Addis Ababa na Habasha a ƙarshen watan Augusta, inda ya samu halartar ministocin makamashi na ƙasashen nahiyar, domin tattauna hanyoyin samar da mafita mai ɗorewa ga ƙarancin makamashi a nahiyar, ta hanyar amfani da albarkatun hasken rana.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha