Masana sun yi Allah wadai da yunƙurin Amurka na neman daƙile cigaban al’ummar Xinjiang

Daga CMG Hausa

Kwararrun masanan ƙasar Sin sun soki lamirin ‘yan siyasar ƙasar Amurka masu adawa da ƙasar Sin, wadanda ke shirya maƙarƙashiya domin hana al’ummar yankin Xinjiang damamamkinsu na cigaba ta hanyar yaɗa ƙarairayin cewa, wai ana tilasta aikin kwadago a shiyyar.

Sun yi Allah wadan ne a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’ar da ta gabata a Urumqi, babban birnin jahar Xinjiang mai zaman kanta ta Uygur ta ƙasar Sin.

Cao Wei, wani shehun malamin jami’ar Lanzhou, ya bayyana cewa, sakamakon fargabar kakaba takunkumi daga ƙasar Amurka, ya sa wasu daga cikin kamfanoni ba su son daukar ma’aikatan ƙwadago ‘yan ƙabilar Uygur, inda hakan ke haifar da ƙaruwar rashin ayyuka yi da kuma koma bayan cigaban yanayin zaman rayuwar al’ummar Uygur.

Shi ma Ildos Murat, mataimakin shugaban tarayyar ƙungiyoyin ‘yan kasuwan yankin Xinjiang, ya bayyana cewa, gaskiyar magana shi ne, Amurka ita ne ƙasar da har yanzu ayyukan ƙwadago na tilas ke cigaba da wanzuwa har a wannan ƙarni na 21, yayin da ‘yan cin rani su ne matsalar ta fi shafa, kuma gwamnatin Amurka ta kawar da kanta daga sauke nauyin dake wuyanta wajen ba su kariya.

Fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *