Masanan ƙasa da ƙasa: Ba za a yarda Japan ta musunta tarihin kai hari ba

Daga CMG HAUSA

Ƙasar Japan ta sanar da mika wuya ba tare da gindaya sharaɗi ba a ranar 15 ga watan Agustan shekarar 1945, amma wasu ‘yan ƙasar sun musunta tarihin ƙasar na kai hari, kan wannan batu, masanan wasu ƙasashen Asiya sun bayyana cewa, ra’ayinsu yana da hadari, kuma ba zai yiwu a yarda ba.

Shahararren masanin dake aiki a kafar watsa labarai, ɗan asalin ƙasar Malaysia dake rayuwa a ƙasar Singapore Zhong Tianxiang yana mai cewa, mutane da yawan gaske sun rasa rayuka sakamakon harin da sojojin ƙasar Japan suka kai yayin yakin duniya na biyu, wannan haƙiƙanin abu ne na tarihi, wanda ba zai yiyu a musunta ba, musamman ma a ƙasashen Asiya. Kowace shekara mun saba da tunawa da alhinin waɗanda suka rasu yayin yakin domin jaddada cewa, bai kamata a manta da tarihi ba.

Idan Japan ta musunta tarihi, har ta gyara abubuwan da aka rubuta kan batun cikin litattafan ɗaliban makarantar ƙasar, ba zai yiyu a yarda ba, saboda matakan da suka ɗauka aikata laifi ne.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa