Masanin hulɗar ƙasa da ƙasa a Jami’ar Abuja: Ƙasar Sin na sa ƙaimi ga sabon nau’in dunƙulewar duniya

Daga CMG HAUSA

Shugaban sashen ilimin siyasa da hulɗar ƙasa da ƙasa a jami’ar birnin Abuja dake tarayyar Najeriya Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce ƙasar Sin ta ba da gudummawa mai kyau, ga sabon nau’in tsarin dunƙulewar duniya, da gudanar da harkokin mulki a duniya, kuma tana daya daga cikin masu sa kaimi ga sabon tsarin duniya.

Sheriff Ghali Ibrahim, ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da manema labarai a baya-bayan nan.

Shaihun malamin ya ce an daɗe ana aiwatar da dunƙulewar duniya, bisa jagorancin ƙasashen yamma, da nufin inganta tsarin siyasa, da tsarin tattalin arziki, da akidu, da al’adu irin na ƙasashen yamma a duk faɗin duniya, domin cin gajiyar dukkanin duniya, kuma yawancin ƙasashen Afirka, da sauran ƙasashe masu tasowa, ba sa iya cin gajiyar irin wannan tsari na dunƙulewar duniya.

Dangane da maganar “raba gari da ƙasar Sin ta fannin tattalin arziki”, da wasu cibiyoyi da ‘yan siyasar yammacin duniya suka kira a yi a baya-bayan nan, Farfesa Ghali ya yi nuni da cewa, hakan na faruwa ne, kawai saboda ba za su amince da cewa, ƙasar Sin na samun bunƙasuwa cikin sauri ba, kuma suna fargabar cewa, nasarar da Sin ta samu za ta zama abin koyi ga sauran ƙasashe masu tasowa, wanda hakan zai girgiza ikonsu na mallakar moriyar duniya.

Farfesa Ghali ya ƙara da cewa, shigar da ƙasar Sin cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya, muhimmin taimako ne ga ci gaban tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa irinsu Najeriya, kuma shawarar “Ziri daya da hanya ɗaya” da ƙasar Sin ta gabatar, na ci gaba da taimakawa ƙasashe masu tasowa, wajen inganta ababen more rayuwa da ake buƙata, domin samun ci gaba.

Kazalika babbar kasuwar ƙasar Sin da ke buɗe kofa ga ƙasashen waje, tana da matukar jan hankalin ƙasashe masu tasowa. Ghali ya jaddada cewa, maganar “raba gari da ƙasar Sin ta fannin tattalin arziki”, ba za ta samu amincewa daga ƙasashe masu tasowa ba, saboda hakan na nufin raba gari da samun ci gaban su.

A cewar masanin, “Idan babu ƙasar Sin, ba za a samu zarafi na ci gaba da yunƙurin dunƙulewar duniya ba”.

Mai fassara: Bilkisu Xin