Masanin Nijeriya: Sin aminiyar ƙasashen Afirka ce a kodayaushe

Daga CMG HAUSA

An kira taron masu shiga tsakani na tabbatar da sakamakon taron ministoci karo na 8 na dandalin taron tattauna haɗin gwiwar dake tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen Afirka a ranar 18 ga wannan wata ta kafar bidiyo, inda shehun malami a cibiyar nazarin yadda ake daidaita rikici da wanzar da zaman lafiya ta tarayyar Najeriya, Oboshi Agyeno ya bayyana yayin da yake zantawa da wakilinmu na CMG cewa, sakamakon da aka cimma a jere yayin taron sun nuna cewa, a ko da yaushe ƙasar Sin ta kasance babbar aminiya ga ƙasashen Afirka.

Oboshi Agyeno ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta dade tana nacewa kan manufar “ƙasashen Afirka su daidaita matsala ta hanyar da ta dace da su”, kuma har kullum tana taimakawa ƙasashen Afirka yayin da suke tsara hanyar daidaita matsalar, abubuwan da suka shaida cewa, kasar Sin aminiyar ƙasashen Afirka ce a ko da yaushe.

Oboshi Agyeno ya ƙara da cewa, ya dace masu tsara manufofi da ‘yan siyasa da sauran masana masu ruwa da tsaki, su yi ƙoƙari domin ingiza hulɗar dake tsakanin Sin da Afirka ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire, ta yadda za a gina kyakkyawar makomar Sin da Afirka a sabon zamanin da ake ciki, tare kuma da ciyar da tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Afrika gaba, da kyautata rayuwar al’ummomin Afirka yadda ya kamata.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa