Masarautar Zazzau ta dakatar da Hakimi kan zargin lakaɗa wa matashi duka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Masarautar Zazzau ta dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah daga kujerarsa ta Marafan Yamman Zazzau.

Masarautar ta ce ɗaukar matakin ya biyo bayan koken da al’ummar Unguwar Magajiya da ke birnin Zariya suka miƙa, na zargin cin zarafin wani mutum da ake yi wa basaraken.

A takardar sanarwar da mai magana da yawunta, Abdullahi Aliyu Ƙwarbai ya fitar ranar Talata, masarautar ta ce ta amince cikin gaggawa ta dakatar da Hakimin har sai abin da hali ya yi a nan gaba.

Shi dai Alhaji Mustapha, majalisar ta same shi ne da laifin zartar da hukunci kan wani Yusuf Yahaya mazaunin Unguwar Magajiya wanda a bisa doka ba shi da ba shi da damar yi ko ɗaukan haka, a cewar sanarwar.

Masarautar ta kuma jawo hankalin dukkan Hakimai da Dagatai da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya cewar ba ta amince da su rinƙa ɗaukar doka a hannunsu ba.

Majalisar Masarautar ta umarci masu riƙe da sarautu da su kiyaye cewan ba za ta lamunce da cin zarafi ko tozarta kowane irin jinsi na al’umma ba. Ta kuma ƙara jawo hankalin da a rinƙa miƙa waɗanda ake tuhuma bisa laifuka ga mahukunta.

Majalisan Masarautar ta kuma tabbatar wa al’umma cewar a shirye take domin ɗaukar mataki mai tsanani ga duk wanda ya saɓa wa dokokin da shari’a ta shimfiɗa.

Sai dai da yake mayar da martani kan dakatarwar, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah ya ce ya sa an daki shi wanda ake zargin ne saboda ya kama shi yana luwaɗi da wani yaro a bayan gidansa.

Ya kuma zargi wasu ’yan majalisar Sarki da hannu wurin ta’azzara wannan rikicin.

A cewar shi, ya ɗauki wannan matakin ne don gudun vata sunan shi da na Sarkin Zazzau.

Ya buƙaci a gabatar da shi ga hukuma maimakon dakatar da shi da aka yi kawai, ba tare da binciken abin da ya sa ya ɗauki wannan matakin ba.

Don haka wannan matakin da aka ɗauka an biye wa son zuciyar wasu ne kawai, a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *