Masarautar Zazzau ta naɗa ɗanjarida a matsayin Ɗan Iiyya

Daga WAKILIN MU

Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya naɗa Alhaji AbdulRahaman Nuhu Bayero a matsayin sabon Ɗan Iyyan Zazzau.

AbdulRahaman Nuhu Bayero ya maye gurbin marigayi Ɗan Iyan ne wanda ya rasu a Nuwamban 2020.

Wasiƙar naɗin wadda ta sami sa hannun Sakataren Sarkin Zazzau kuma Sarkin Fulanin Zazzau, Alhaji Barau Musa Aliyu, ta nuna kwamitin naɗi zai sanar da ranar da bikin naɗin zai gudana.

Masarautar ta taya AbdulRahaman Nuhu Bayero murnar samun wannan muƙami tare da addu’ar Allah ya taimaka masa.

Sabon Ɗan Iyyan, ma’aikaci ne a sashen labaru da al’amuran yau a babban ofishin Radio Nigeria da ke Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *